An kashe ’yan bindiga 5 da ceto mutum 32 a Katsina

Jami’an tsaro sun gudanar da samame a sansanin wani sanannen jagoran ’yan bindiga mai suna Muhammad Fulani, wanda aka ce yana gudanar da ayyukansa a yankunan Matazu da Musawa da Kankia da Charanchi da kuma wasu sassan maƙwabciyarsu Jihar Kano.

An kashe ’yan bindiga 5 da ceto mutum 32 a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta tsananta daƙile ayyukan ’yan bindiga, inda jami’an tsaron haɗin gwiwa suka kashe mutane biyar da ake zargin ’yan bindiga ne, sannan suka ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su a sassan jihar.

Ayyukan tabbatar da tsaron, waɗanda ya haɗa da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka gudanar, sun nufi sansanin wani sanannen jagoran ’yan bindiga mai suna Muhammad Fulani, wanda aka ce yana gudanar da ayyukansa a yankunan Matazu da Musawa da Kankia da Charanchi da kuma wasu sassan maƙwabciyarsu Jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin Gida na Jihar, Dakta Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun kuma ƙwato bindiga ɗaya ƙirar AK-47, da ƙunson harsasai guda 10 na da kuma babura tara waɗanda ake zargin ƙungiyar masu aikata laifin na amfani da su.

A cewar sanarwar, ɗaya daga cikin ’yan bindigar da aka kashe yayin samamen an gano da aka fi sani da Samagi, wanda aka ce na hannun damar wani gagarumin ɗan bindiga ne mai suna Muhammadu Kachalla.

Haka kuma, Kwamishinan ya bayyana cewa samamen ya kai ga ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da mata 10, maza tara, da kuma yara 13 da ’yan bindigar ke tsare da su.

Mu’azu ya nanata cewa, gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda tana nan kan matsayarta na rashin tattaunawa da ’yan bindiga, yana mai jaddada cewa gwamnatin ta ƙuduri aniyar kakkaɓe ayyukan ’yan bindigar a faɗin jihar.

“Gwamna ya daɗe yana bayyana cewa, gwamnatinsa ba za ta yi sasantawa da ’yan bindiga ba, maimakon haka za ta ci gaba da ɗaukar ƙwararan matakai da nufin kawar da ayyukan ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya a Jihar Katsina,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa, har yanzu ana ci gaba da farautar Muhammad Fulani da sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da matsa lamba a maɓoyar masu laifi a faɗin yankunan da abin ya shafa.