An kashe ‘yan Boko Haram ‘100’a Kamaru
A shekaranjiya Laraba ne Ministan Tsaron Jamhuriyar Kamaru ya ce dakarun sojin kasar sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram guda100 a wani samame da suka kai musu, kamar yadda BBC ta bayyana.Joseph Beti Assomo, wanda ya bayar da sanarwar a gidan talabijin na kasar, ya ce dakarun sun ceto mutane 900 da ‘yan Boko Haram […]
A shekaranjiya Laraba ne Ministan Tsaron Jamhuriyar Kamaru ya ce dakarun sojin kasar sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram guda100 a wani samame da suka kai musu, kamar yadda BBC ta bayyana.
Joseph Beti Assomo, wanda ya bayar da sanarwar a gidan talabijin na kasar, ya ce dakarun sun ceto mutane 900 da ‘yan Boko Haram din suka yi garkuwa da su.
Sanarwar ta ce, “An gudanar da samame na musamman domin kakkabe ‘yan Boko Haram tsakanin ranakun 26 zuwa 28 ga watan Nuwamba a kan iyakarmu da Najeriya, kuma an kashe ‘yan Boko Haram 100.”
Ya ce sun kwato makamai da alburusai da dama, sannan suka samu tutocin kungiyar IS a wurin da suka kai samamen, kodayake bai yi karin bayani ba tukuna.
Har ila yau, wannan ya faru ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga biyu suka kai hari a arewacin kasar a daren ranar Talata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla uku.
Hakazalika, an kai makamancin wannan harin a garin Waza da ke da yankin Arewa-mai-Nisa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida – ciki har da maharan guda uku.
Jami’an tsaro sun kashe ‘yar kunar bakin wake ta uku a yayin da take kokarin tayar da bam din da ke jikinta.