An kashe ’yan Boko Haram 143 a Kamaru

Sakamakon harin da ’yan kungiyar Boko Haram suka kai ranar Litinin, a garin Kolofata da yake makwabtaka da Najeriya a Lardin Arewa-mai-nisa na kasar Kamaru, kakakin Gwamnatin kasar Minista Issa Tchiroma Bakary a wata sanarwar da ya fidda ya tabbatar da mutuwan soja guda daga cikin dakarun tsaro na Kamaru da kuma wasu hudu da […]

An kashe ’yan Boko Haram 143 a Kamaru
An kashe ’yan Boko Haram 143 a Kamaru

Sakamakon harin da ’yan kungiyar Boko Haram suka kai ranar Litinin, a garin Kolofata da yake makwabtaka da Najeriya a Lardin Arewa-mai-nisa na kasar Kamaru, kakakin Gwamnatin kasar Minista Issa Tchiroma Bakary a wata sanarwar da ya fidda ya tabbatar da mutuwan soja guda daga cikin dakarun tsaro na Kamaru da kuma wasu hudu da suka jikkata a yayin da ’yan kungiyar Boko Haram 143 suka rasa rayukansu.

bangarorin biyu sun debi tsawon sama da sa’o’i biyar suna yin musayar harbe-harbe bayan dirar mikiyar da maharan suka yi da jijjifi, da yunkurin neman mamaye barikin sojoji na garin Kolofata.
Minista Issa Tchiroma Bakary ya kora alhakin kai wannan harin akan kungiyar Boko Haram wadanda ya ce sun fito daga Najeriya. Ya ce sun yi hakan ne da zummar yi wa barikin sojojin kawanya. A lokacin harin sun yi amfani da gajimare da yake shamakantar da mutane a wannan lokaci gabannin su yi kutse. Maharan a fadin kakakin gwamnatin da yawansu ya kama daruruwa sun samu ketare iyaka ne suka yi wa dakarun tsaro shigar sauri, sai dai duk da haka dakarun sun samu mayar da maharan baya zuwa kan iyakan Kamaru da Najeriya. Ya ce wannan adadin shi ne ma fi muni da kungiyar Boko Haram ta yi.
Sai dai wasu masana sun ce wannan lokacin ba na lissafa adadin dimbin asarar rayukan jama’a da ake haddasa wa kungiyar Boko Haram ba ne, face hankaltuwa da irin hadarurrukan da suke tattare ga kungiyar. Hakan ya kai ga wasu rahotanni bayyana cewa a yanzu haka kasar Chadi na tuna hanyoyin da itama za ta bi wurin fara yin rigakafi game da irin hare-haren kungiyar take kaiwa a kasashe makwabtan Najeriya. Hakan ya kaita ga matakin farko sanya matakan tsaro akan iyakokinta da Najeriya a cikin tafkin Chadi. Wani kaulin kuma na cewa suka yi ta rufe iyakokin nata da Najeriya.
Hakannan ma a makon da ya gabata wani soja guda ne ’yan kungiyar suka harbe a lokacin da yake daf da shiga garin Kolofata wurin kai kayan bukata ga sauran dakarun da suke garin bayan ya taso daga garin Mora. A irin wannan halin ne Shugaban kasa Paul Biya ya yi kira ga kasashen Yammacin Duniya da su yi taron gano wurin yaki da ta’addaci da kuma bude yaki ba tare da wani jinkiri ba ga kungiyar Boko Haram. Wannan ya biyo bayan sakon a cikin fefen bidiyo da Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya aika wa Shugaba Biya, inda ya ja hankalinsa da ya yi hatara. Ya ce idan bai sauya yadda yake tafiyar da mulki ba, to fa kasarsa ka iya zama tankar yankin Arewa-maso-Gabashin Najeriya.