An kashe ‘yan gudun hijira 13 a Borno
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mayakan kugiyar Boko Haram sun kai hari garin Kofa da ke karamar Hukumar Konduga ta jihar Borno a daren Alhamis tare da afkawa sansanin ‘yan gudun hijira na garin. Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin a safiyar yau Alhamis ya ce, akalla fararen hula 13 aka kashe a harin yayin […]
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mayakan kugiyar Boko Haram sun kai hari garin Kofa da ke karamar Hukumar Konduga ta jihar Borno a daren Alhamis tare da afkawa sansanin ‘yan gudun hijira na garin.
Wakilinmu wanda ya ziyarci yankin a safiyar yau Alhamis ya ce, akalla fararen hula 13 aka kashe a harin yayin da aka kona dakunan wucin gadi sama da 40 a sansanin ‘yan gudun hijira na Dalori.
Majiyarmu ta binciko cewa, a yanzu haka wasu ‘yan gudun hijira a sansanin sun bace.