An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato
’Yan gudun hijirar da suke garin Sabon Birni da Isa, amma saboda wahala sun sake komawa ƙauyensu.
Fulani fiye da 3,000 na gudun hijira a Kudancin Kaduna
’Yan bindiga sun keshe ’yan gudun hijira uku sun yi garkuwa da wani a ƙauyen Gangara cikin ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
Waɗanda aka kashen suna cikin ’yan gudun hijirar da suka bar ƙauyensu domin ya zama kufai, don su riƙa samun abinci ganin an ƙyale su can ana ta kai masu farmaki.
’Yan gudun hijirar da suke garin Sabon Birni da Isa, amma saboda wahala sun sake komawa ƙauyensu.
ɗaya daga cikinsu ya sanar da wakilinmu su kusan 200 suka koma ƙauyen nasu na Gangara a ranar Laraba da ta gabata, ashe ’yan bindigar suna wuraren sun ɓoye a nan ne suka buɗe masu wuta.
Ya ce, a lokacin da suna tsalka gulbin na kusa da ƙauyensu ne ’yan bindigar suka kai masu farmaki hakan ya sa da yawa wasu sun gudu.
“Mutum uku sun mutu a lokacin da suke yunkin tsallako gulbin, a ruwan suka faɗa ya kuma tafi da su ba gawar da aka ɗauko a gulbin.”
Waɗanda suka rasu sun haɗa da: Hurera Halilu uwa ce da ta bar yara bakwai, da Hassan Haruna da Sani Musa.
Majiyar ta ce, haka kuma ’yan bindigar sun yi garkuwa da Muhammad Malam Bakwai.
Ya ce, ’yan gudun hijirar ba su so dawowa ƙauyen ba, saboda ɗan bindigar nan Kacalla Jamau Baki da ke da ƙawance da Bello Turji an ce ya faɗi duk wanda ya samu a ƙauyen nan sai ya kashe shi.
Shugabannin ƙauyen sun soki gwamnati kan rashin bada wani taimako da gudunmuwa da suke kai masu hasalima ba wani jami’in gwamnati da ya ziyarce su.
Duk yunƙurin jin tabakin rundunar ’an sandan jiha bai yi nasara ba, saboda jami’in hulɗa da jama’a DSP Ahmad Rufa’i bai kusa ga waya a lokacin da aka kira da tura masa saƙon kar takwana.