An kashe ’yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu
A shekarar 2008, sama da mutane 60 ne suka mutu a irin wannan rikicin ƙin jinin baƙi a Afirka ta Kudu.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar cewa an kashe ’yan ƙasarta biyu a watan da ya gabata a Afirka ta Kudu, sakamakon zanga-zangar ƙin jinin baƙi da ake yi a ƙasar.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa ta bayyana a ranar Lahadi cewa an kashe mutanen ne a ranar 28 ga Yuni, kwanaki biyu kafin wa’adin da masu zanga-zangar suka sanya ba bisa ƙa’ida ba na cewa baƙi su fice daga ƙasar.
- PDP ta caccaki Gwamnan Gombe kan bai wa mawaƙin Kano kyautar mota da filaye
- FIFA ta janye dakatarwar da ta yi wa ɗan wasan Amurka Folarin Balogun
Sanarwa ta bayyana sunayen mutanen biyu — Emeka Charles Iroegbu da Musa Yunana Joe — waɗanda ’yan sandan lardin Tshwane suka kashe rana guda a wurare daban-daban.
Sai dai har zuwa yanzu, rundunar ’yan sandan Afirka ta Kudu ba ta fitar da wata sanarwa ko mayar da martani kan lamarin ba.
A watan Afrilu da Mayu, masu zanga-zangar sun zargi baƙi da haddasa matsalar rashin aikin yi, ƙaruwar aikata laifuka da kuma matsin lamba kan ayyukan gwamnati.
Wannan tashin hankali ya sa ƙasashen Najeriya, Ghana da Malawi suka kwashe wasu daga cikin ’yan ƙasashensu da ke zaune a Afirka ta Kudu, tare da kiran jakadunsu domin tattaunawa.
A shekarar 2008, sama da mutane 60 ne suka mutu a irin wannan rikicin ƙin jinin baƙi a Afirka ta Kudu, lamarin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka bayyana a matsayin hare-haren ƙin jinin baƙi.