An kashe ’yan sa-kai 9 a Sakkwato

Ƙaramar Hukumar Isa ta kasance tungar ‘yan ta’adda kuma tana da matuƙar haɗari ga jami’an tsaro.

An kashe ’yan sa-kai 9 a Sakkwato

Aƙalla jami’an tsaron sa-kai na Civilian JTF tara da ke yaƙi da ‘yan bindiga a Jihar Sakkwato ne aka kashe a wani harin kwantan ɓauna da aka kai musu, yayin da wasu da ba a tantance adadinsu ba suka samu raunuka daban-daban.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu jami’an na CJTF uku.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata a Ƙaramar Hukumar Isa ta jihar.

Majiyar daga CJTF ta ƙara da cewa Ƙaramar Hukumar Isa ta kasance tungar ‘yan ta’adda kuma tana da matuƙar haɗari ga jami’an tsaro.

“Mun rasa mambobinmu tara a wani harin kwantan ɓauna da aka kai a Ƙaramar Hukumar Isa.

“Wasu da dama sun samu raunuka, an kuma yi awon gaba da wasu guda uku a harin bayan da mambobinmu suka amsa kiran gaggawa don tallafa wa jami’an tsaro.

“Mun samu labarin baƙin ciki kwanaki biyu da suka wuce. Tun farkon wannan shekara da gwamnatin jihar ta buƙaci mu tura mambobinmu domin tallafa wa sojoji a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.”

Ana iya tuna cewa, wannan shi ne karo na biyu da ‘yan bindiga za su yi wa jami’an CJTF kwanton ɓauna a Jihar Sakkwato a cikin watanni biyu.

Tags