An kashe ‘yan sanda 108 a cikin wata 8 a Najeriya
Bayan harin da wasu matasa suka kai wa ‘yan sanda a College Road da ke yankin Ifako Ijaiye da ke Jihar Legas, inda suka kashe wasu ‘yan sanda. Aminiya ta gano cewa a cikin wata 8 da suka wuce, akalla ‘yan sanda 108 aka kashe a irin wannan harin. A kididdigira Aminiya, ta gano cewa […]

Bayan harin da wasu matasa suka kai wa ‘yan sanda a College Road da ke yankin Ifako Ijaiye da ke Jihar Legas, inda suka kashe wasu ‘yan sanda. Aminiya ta gano cewa a cikin wata 8 da suka wuce, akalla ‘yan sanda 108 aka kashe a irin wannan harin.
A kididdigira Aminiya, ta gano cewa yawancin ‘yan sanda ‘yan ta’adda ne ke musu kisar gilla, yayin da wasu kuma direbobi ne ke kashe su, sai kuma wasu lokutan da ake samun dan sanda ya kashe abokin aikinsa.