An kashe ‘yan sanda 2 a Saudiyya

A shekaranjiya Laraba ne aka harbe wasu ’yan sanda har lahira a kasar Saudiyya lokacin da aka kai wa wata motar da suke ciki hari, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya bayyana. Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a tabbatar ko su wanene suka kai harin da ya faru a gabashin yankin […]

An kashe ‘yan sanda 2 a Saudiyya
An kashe ‘yan sanda 2 a Saudiyya

A shekaranjiya Laraba ne aka harbe wasu ’yan sanda har lahira a kasar Saudiyya lokacin da aka kai wa wata motar da suke ciki hari, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya bayyana.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a tabbatar ko su wanene suka kai harin da ya faru a gabashin yankin katif ba.
An dade ana samun tarzoma tsakanin jami’an tsaro da tsirarun Musulmi mabiya darikar Shi’a da ke wannan yankin.
Al’umomin yankin sun sha korafin cewa an mayar da su saniyar ware, kuma a yanzu ‘yan sanda sun bazama neman wasu da ake zargi na da alaka da wata zanga-zanga da aka yi a yankin a shekarar 2011.
Kodayake, a watan jiya wata kungiya a yankin wadda ta ce tana da dangantaka da kungiyar ISIS ta bayyana cewa ita ce ta kai wani hari a wani masallacin ’yan Shi’a, inda mutum biyar suka mutu, wasu guda tara kuma suka ji raunuka.