An kashe mutum 5 a rikicin ‘yan sanda da ‘yan shi’a a Abuja

A kalla mutum biyar ne aka kashe ciki harda Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda (DCP), Usman Umar wanda ke aiki a shiyyar birnin tarayya Abuja, da wasu a rikicin da aka yi lokacin da mabiya mazhabar Shi’a suke zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky jiya Litinin. An kashe Jami’in dan sandan ne lokacin da […]

An kashe mutum 5 a rikicin ‘yan sanda da ‘yan shi’a a Abuja

A kalla mutum biyar ne aka kashe ciki harda Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda (DCP), Usman Umar wanda ke aiki a shiyyar birnin tarayya Abuja, da wasu a rikicin da aka yi lokacin da mabiya mazhabar Shi’a suke zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky jiya Litinin.

An kashe Jami’in dan sandan ne lokacin da yake kokarin tabbatar da doka da kuma kadarorin gwamnati.