An kashe ’yan ta’adda 624, an kama 1,051 a watan Mayu — DHQ
Sojoji sun kuɓutar da mutane 386 da aka yi garkuwa da su sama da shekaru 10.
Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa sojojin sun kashe ‘yan tada ƙayar baya aƙalla 640, sun kuma kama mutane 1,051 da ake zargi da ta’addanci tare da kuɓutar da mutane 563 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Mayu.
Daraktan kula da ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ƙoƙarin da sojojin Najeriya ke yi a ranar Alhamis a Abuja.
Buba ya bayyana cewa, sojojin sun kama wasu da ake zargi da suka haɗa da masu kawo musu makamai da masu ba da bayanai.
Ya ƙara da cewa, sojojin sun kuma ƙwato makamai iri-iri har guda 707 da alburusai 16,487 da suka haɗa da bindigogi ƙirar AK47 411, da bindigogi ƙirar gida guda 234 da kuma manyan bindigogi guda 43 da dai sauransu.
A shiyyar Arewa maso Gabas, Buba ya ce rundunar Operation Haɗin Kai ta samu gagarumar nasarar gudanar da ayyukansu ta hanyar kawar da wasu manyan ‘yan tada ƙayar baya da suka haɗa da wani Malam Mohammed, jagoran masu tada ƙayar baya a dajin Sambisa.
Sai dai ya bayyana cewa sojojin sun kuɓutar da mutane 386 da aka yi garkuwa da su sama da shekaru 10, yana mai cewa an miƙa waɗanda abin ya shafa ga gwamnatin jihar Borno.
“A cikin wannan watan, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 306, sun kama mutane 199 da ake zargi da kuma ceto wasu 219 da aka yi garkuwa da su.”