An kashe ‘yan ta’adda sama da 9,000 cikin shekara ɗaya — Minista
Ministan ya ce cikin shekara guda hukumomin tsaro a Najeriya sun samu gagarumar nasara.
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce hukumomin tsaron Najeriya sun kashe aƙalla ’yan bindiga da ’yan tada ƙayar baya 9,300 cikin shekara guda.
Badaru, ya kuma ce an cafke aƙalla mutum 1,437 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, inda ya ƙara da cewa sojoji sun kashe mutum 363 a shekarar da ta wuce, a ƙoƙarinsu na bunƙasa harkar haƙo man fetur a ƙasar nan.
- An rantsar da Mahamat Deby a matsayin Shugaban Chadi
- Sanusi II ne Sarki ɗaya tilo a Kano — Gwamna Abba
Ministan ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis, a yayin wani taron ministocin Najeriya, inda ya bayyana ayyukan ma’aikatarsa kamar yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya umarta.
Tsohon gwamnan na Jihar Jigawa, ya bayyana cewa an samu nasarar hakan ne biyo bayan haɗin gwiwa tsakanin rundunar sojin ƙasar nan da suka haɗa da sojin ruwa da na sama da kuma sauran jami’an tsaro.
A cewarsa, rundunar sun yi aiki tare da haɗin gwiwa, wanda hakan ya samar da nasarori masu tarin yawa cikin shekara guda da shugaba Bola Tinubu ya karɓi ragamar mulki.
“Babban hafsan hafsoshin sojoji, hafsan sojin ruwa, da hafsan sojin sama suna aiki saɓanin yadda suka saba yi a baya. Hakan ya haifar da ci gaba a ayyukansu.
“Bugu da ƙari, muna da haɗin gwiwa tare da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ‘yan sanda, NSCDC, da duk sauran hukumomin tsaro,” in ji Badaru.
Da yake ƙarin haske, ministan ya bayyana cewa an ƙwato makamai sama da 4,000 daga hannun masu aikata laifuka.
Ya ƙara da cewa a sakamakon ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da satar mai, “mafi yawan matatun mai ba sa aiki, duk sun lalace.”
Ya ƙara da cewa, “Wannan (haɗin kai) ya haifar da gagarumin ci gaba cikin shekarar da ta gabata. Saboda haɗin kai, mun samu damar kawar da ‘yan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya fiye da 9,300; sannan an kama kimanin 7,000, yayin da kuma aka kuɓutar da mutum 4,641 waɗanda aka sace cikin shekara guda kacal.
“Mun kuma ƙwato makamai 4,882 da alburusai 83,900 cikin shekara ɗaya. Daga cikin waɗanda muka kawar su ne ‘yan bindiga kamar yadda kuka ji. Mun kashe shugabanin ‘yan bindiga aƙalla 20 waɗanda ke jagorantar ayyukan ‘yan ta’adda cikin shekara guda kacal.”