An kashe ’yar shekara uku ta hanyar fyade
A safiyar ranar Talata da ta gabata ce aka tsinci gawar wata karamar yarinya mai kimanin shekara uku mai suna Khadija a makararantar Islamiyyar da mahaifiyarta ke koyarwa a unguwar Walalambe a karamar Hukumar Nasarawa da Jihar Kano. Mahaifin marigayiyar Malam Abubakar Abdullahi wanda aka fi sani da IBB, ya shaida wa Aminiya cewa marigayiya […]

A safiyar ranar Talata da ta gabata ce aka tsinci gawar wata karamar yarinya mai kimanin shekara uku mai suna Khadija a makararantar Islamiyyar da mahaifiyarta ke koyarwa a unguwar Walalambe a karamar Hukumar Nasarawa da Jihar Kano.
Mahaifin marigayiyar Malam Abubakar Abdullahi wanda aka fi sani da IBB, ya shaida wa Aminiya cewa marigayiya Khadija ta bata ne lokacin da suka tafi makarantar Islamiyya da ’yan uwanta. “A ranar da lamarin ya faru mahaifiyarta ba ta samu zuwa makarantar ba saboda zazzabin da ke damunta sai ta tafi da ’yan uwanta maza biyu wadanda daga baya suka dawo gida suka gaya mana cewa bayan an tashi daga makarantar da misalin karfe 5:30 na yamma sun nemi Khadija sun rasa,” inji shi.
Ya ce: “Hakan ya sa muka koma makarantar don duba ta amma ba mu gan ta ba sai bayan kwana hudu aka kira mu aka ce an gan ta a makarantar a cikin wani karamin ofis.”
Mahaifin yarinyar ya ce da ya je sai ya ga gawarta tsirara kuma jini yana fitowa daga gabanta, gawar babu kyan gani domin ta fara wari, “Hakan ya sa ba mu ko taba ta ba, muka kira ’yan sanda suka dauki gawar sun tafi da ita don gudanar da bincike daga bisani suka dawo mana da gawar don yi mata sutura,” inji shi.
Malam Abubakar ya yi kira ga Rundunar ’Yan sandan Jihar ta binciko wadanda suka yi wannan aika-aika tare da hukunta su. “Duk da cewa Khadija ta rasu to amma muna neman a bi mana hakkinmu, kuma akwai bukatar gwamnati ta dauki mataki, saboda idan aka bar abin hakan nan to Allah ne kadai Ya san inda lamarin zai tsaya,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yanzu haka sun fara gudanar da bincike a kan lamarin har sun kama mutum tara wadanda mafi yawansu malaman makarantar Islamiyyar da aka tsinci gawar marigayiyar ce. Majiya ya cewa ana zargin an kashe yarinyar ce ta hanyar fyade lura da yadda aka samu jini a jikinta, kuma ya tabbatar wa iyalan marigaiyar cewa za su iya kammala bincikensu a cikin kwana hudu saboda suna samun ci gaba a bincikensu.