An kashe yawancin hakimaina a rikicin Boko Haram —Shehun Borno
Basaraken ya bayyana hakan ne a yayin da Laftanar-Janar Olukoyede ya kai ziyarar aiki a fadarsa da ke Maiduguri tare da tawagarsa.
Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ya tabbatar wa sabon Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, goyon bayansa wajen kawo ƙarshen rikicin Boko Haram da aka daɗe ana gwabzawa a yankin.
Basaraken ya bayyana hakan ne a yayin da Laftanar-Janar Olukoyede ya kai ziyarar aiki a fadarsa da ke Maiduguri tare da tawagarsa.
Shehun Borno ya kara cewa, dukkan shugabannin gargajiya da ke ƙarƙashinsa za su hada kai da sojoji domin fallasa duk wani mai alaka da ta’addanci a jihar.
“An kashe yawancin hakimaina da wasu iyaye da dama a cikin wannan rikici, ni ma da kyar na tsira daga harin kunar bakin wake a kan hanyata daga masallaci zuwa cikin fada, wanda an kai min harin ne kawai saboda ina ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro don tilasta bin doka.
- ’Yan sanda sun ceci matafiya 20 daga hannun ’yan ta’adda a Katsina
- Shugabanci: ’Yan Arewa su jira sai 2031 —Akume
“Har yanzu kuwa ina kan bakata a koyaushe wajen fallasa duk wani ko wasu masu kokarin aikata ta’addanci a cikin al’ummominmu,” in ji shi.
A nasa jawabin, Laftanar-Janar Oluyede ya gode wa Shehun Borno kan rawar da yake takawa wajen taimaka wa ayyukan yaki da ta’addanci.
“Mai martaba, na zo ne wannan fada mai albarka domin in yi maka gaisuwar ban girma a matsayinka na mahaifinmu, kuma na gode maka da ka taka wannan rawar. Mun samu goyon bayanka tsawon shekaru, musamman wajen taimaka mana wajen ganin mun magance matsalolin ’yan tada kayar baya.
“Ina alfahari da ganinku, kuma mun gode da duk abin da kuke yi tsawon shekaru da kuma goyon bayan da kuke ba mu musamman.”
“Ina sake rokon ka a matsayinka na ubanmu da ka ci gaba da taimaka mana ta wajen zage damtsen mutanenmu domin su ba mu goyon baya don mu kawo karshen wannan tayar da kayar baya; hakan yana da muhimmanci mu kawo karshensa domin jihar Borno ta yi kokari wajen farfado da harkokin tattalin arzikinta.“