An kayar da ’yan Majalisar Wakilai 2 a Ondo
‘Yan majalisar sun nemi yin ta-zarce amma suka sha kaye
Tajudeen Adefisoye (PDP) da Gboluga Ikengboju (APC), ’yan Majalisar Wakilai ne a Jihar Ondo masu neman ta-zarce a zaben 2023, sai dai baki daya ba su kai bantensu ba.
Tajudeen Adefisoye shi ne dan mai wakiltar mazabar Ifedore/Idanre, sannan Gboluga Ikengboju ke wakiltar Okitipupa/Irele na jihar.
- INEC ta ayyana zaben Majalisar Wakilai ‘inconclusive’ a Kogi
- Jam’iyyar LP na neman INEC ta soke zaben Ribas
Adefisoye ya sha kaye ne hannun abokin hamayyarsa na PDP, Festus Akingbaso, a zaben da ya gudana ranar Asabar, a yayin da Ikengboju ya sha kaye a hannun Jimi Odimayo.
A cewar INEC, Adefisoye na APC ya samu kuri’u 20,064, sannan abokin hamayyarsa, Akingbaso, ya samu 24,263.
A hannu guda, Odimayo na Jama’iyyar PDP ya tashi da kuri’u 44,638, Ikengboju kuma 21,066.
A ranar Lahadi INEC ta bayyana Adefisoye da Odimayo a matsayin wadanda suka lashe zabe a yankunansu.