An kera motar alfarma ta katako a kasar bietnam

Wata motar katako da aka kera a kasar bietnam t ashahara a titunjan birnin Ho Chi Minh. Wannan mota da ta yi fice, an kerat ne da managarcin katako, wanda aka kawata shi da zayyana iri-iri. Wanda ya kirkiro ta, wani shugaban kamfanin sarrafa katako ne, wato Le Nguyen Khang, mai kamfanin Binh Duong Le […]

An kera motar alfarma ta katako a kasar bietnam
An kera motar alfarma ta katako a kasar bietnam

Wata motar katako da aka kera a kasar bietnam t ashahara a titunjan birnin Ho Chi Minh. Wannan mota da ta yi fice, an kerat ne da managarcin katako, wanda aka kawata shi da zayyana iri-iri. Wanda ya kirkiro ta, wani shugaban kamfanin sarrafa katako ne, wato Le Nguyen Khang, mai kamfanin Binh Duong Le Lumber.
Ya bayyana wa manema labarai, cewa an fara maganar kera motar ne kamar wasa, a lokacin da suke tattaunawa da wani abokinsa Baturen Ingila da ke aiki a Kamfanin kasuwanci na tafiye-tafiye. An zana fasalin motar tare da taimakon wasu ma’aikatan kamfaninsa mutum 11, ya kuma yi aiki tukuru har na tsawon wata 16 kafin ya kai ga gaci.
An kammala aikin kera wannan mota  cikin watan da ya wuce, kuma da kammala aikin  mai motar ya fara kewaya birni da ita. Mutane na ta damunsa da tambayoyi iri-iri, wasu kuwa so suke yi a dauki hotonsu tare da ita.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda