An kirkiro kwalin taba da ke magana da mashaya

Jami’ar Stirling na gwajin wani kwalin taba da ta kirkiro, don yin gargadi da matasan mata masu zukar taba, amma kwananan za a yi gwajin a kan sauran mutane.Cibiyar bincike da hana shan taba ta jami’ar ta kirkiro na’ukan kwalayen taba masu magana, wadanda aka yi su tamkar katin murnar zagayowar ranar haihuwa. daya daga […]

An kirkiro kwalin taba da ke magana da mashaya
An kirkiro kwalin taba da ke magana da mashaya

Jami’ar Stirling na gwajin wani kwalin taba da ta kirkiro, don yin gargadi da matasan mata masu zukar taba, amma kwananan za a yi gwajin a kan sauran mutane.
Cibiyar bincike da hana shan taba ta jami’ar ta kirkiro na’ukan kwalayen taba masu magana, wadanda aka yi su tamkar katin murnar zagayowar ranar haihuwa. daya daga cikin kwalayen yana bayar da shawara ga masu zukar taba  kan su daina wannan mummunar dabi’a, dayan kuwa cewa yake shan taba na rage kwayoyin haihuwar dan Adam.
Shugabar kungiyar Yaki da shan taba wajen kula da lafiya ta ASH, da ke Scotland, Sheila Duffy, ta ce: Kamfanonin taba ya kamata su sayi wannan sabuwar kirkira, su bazata a kasuwa, don masu shan abin da zai cutar da su, musamman matasa suka shi taitayinsu.”

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda