Majalisar Kano ta kirkiro sabbin masarautu
Sarakunan sabbin masarautun za su kasance masu daraja ta biyu a kuma a karkashin jagorancin Sarkin Kano
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa sabbin masarautu uku da za su kasance masu daraja ta biyu.
Kwanaki 51 ke nan bayan gwamantin jihar mai ci rushe masarautu biyar masu daraja ta daya da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a Jihar.
Dokar da majalisar ta amince da ita a safiyar Talata za ta nada sarakuna masu daraja ta biyu a sabbin masarautun Gaya, Karaye da kuma Rano.
Dokar wadda Mataimakin Shugaban majalisar, Muhammad Bello Bututu, ya gabatar da kudirin ta sanya kananan hukumomi takawa a karkashin sabbin masarautun.
- Umar Bush ya samu mukami a Fadar Shugaban Kasa
- ’Yan bindiga sun kashe mutane 4 sun sace 150 a Zamfara
Masarautar Rano ta ƙunshi kananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya.
Masarautar Gaya ta ƙunshi kananan hukumomin Gaya, Albasu da Ajingi.
Ita kuma Masarautar Karaye ta ƙunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.
Duk sarakunan masarautun za su kasance a karkashin Sarkin Kano kuma za su kasance a matsayin abokan shawararsa.
Amincewa da dokar wadda ke jiran sa hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf, na zuwa ne washegarin da Babbar Kotun Jihar Kano ta umarci tsoffin sarakunan , sarautu biyar na gwamnatin Ganduje daga gabatar da kansu a matsayin sarakunan jihar.
Kotun ta kuma umarci sarakunan rusassun asarautun na Bichi da Gaya da Kanon da Karar da kuma Rano da su dawonda duk kayan gwamnati da ke hannunsu.