An kirkiro sabon maganin ciwon suga
Jami’ar Harbard da ke kasar Amurka ta kirkiro wani sabon maganin ciwon suga. Farfesa Douglas A. Melton ne ya shugabannci ayarin kwararrun masana kiwon lafiya na Jami’ar Harbard wajen samar da sabon maganin. Maganin yana karfafa wa kwayar halitta mai suna insulin da ke taimakawa wajen rage yawan suga a jikin dan Adam, kuma maganin […]
Jami’ar Harbard da ke kasar Amurka ta kirkiro wani sabon maganin ciwon suga.
Farfesa Douglas A. Melton ne ya shugabannci ayarin kwararrun masana kiwon lafiya na Jami’ar Harbard wajen samar da sabon maganin.
Maganin yana karfafa wa kwayar halitta mai suna insulin da ke taimakawa wajen rage yawan suga a jikin dan Adam, kuma maganin zai taimaka wajen magance ciwon suga mai daraja ta daya (Type 1 diabetes).
A rahoton da Mujallar Cell ta buga a ranar 9 ga Oktoba, 2014, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da aka samu magani mai dauke da kwayoyin halittar beta da za su rika taimaka wa jikin dan Adam wajen daidaita yawan suga.
Dokta Henry Osazuwa, wani likitan mata ya ce mutane da yawa suna cewa babu yadda za a warke daga ciwon suga, wanda hakan yake haifar da babbar damuwa ga mata masu juna biyu.
Dokta Osazuwa wanda ya ce ya karanta labarin samun sabon maganin a intanet ne, ya ce ya yi farin ciki da samun wannan magani, sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda maganin zai shafi mata masu juna biyu.
Malam Ahmed Garba wanda ya ce yana fama da ciwon suga tsawon shekara biyu ya ce ba ya da tabbaci maganin zai magance ciwon saboda likitansa ya ce ciwon ba ya da magani sai dai a samu sauki.
Wani mai ciwon wanda bai amince a bayyana sunansa ba, ya ce mahaifansa duka biyu suna fama da ciwon suga, “Wannan ya ba ni kwarin gwiwar al’umma mai zuwa za ta samu hanyoyin magance ciwon suga,” inji shi.
Farfesa Melton, wanda ya jagorancin samar da maganin ya ce ya shafe shekara 20 yana yin nazari kan maganin saboda ’ya’yansa na fama da ciwon suga.