An kirkiro wata waya da za ta taimaka wa manoma gano cututtukan ayaba

Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Duniya a Kasashe Masu Zafi (CIAT) ta ce wadansu masu bincike, sun kirkiro wata sabuwar wayar hannu da za ta taimaka wa manoman ayaba su gano cututtuka biyar da suke damun ayaba. Rahoton cibiyar ya ce an gwada wannan sabuwar waya a kasashen Kolombiya da Jamhuriyar Kongo da Indiya da […]

An kirkiro wata waya da za ta taimaka wa manoma gano cututtukan ayaba

Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Duniya a Kasashe Masu Zafi (CIAT) ta ce wadansu masu bincike, sun kirkiro wata sabuwar wayar hannu da za ta taimaka wa manoman ayaba su gano cututtuka biyar da suke damun ayaba. Rahoton cibiyar ya ce an gwada wannan sabuwar waya a kasashen Kolombiya da Jamhuriyar Kongo da Indiya da Benin da China da kuma Uganda.

Mista Michael Selbaraj jagoran masu binciken da suka kirkiro sabuwar wayar, ya yi bayanin cewa a da manoman ayaba a duniya da suke kokarin kare gonakin ayabarsu daga cututtuka ba su da cikakken sani kan yadda za su kare gonakin nasu.

Ya ce amma yanzu sun samu dama idan suka yi amfani da sabuwar wayar wajen lura tare da magance cututtukan ayabar.

Rahoton ya yi bayanin cewa ayaba tana daya daga cikin fitattun kayayyakin lambu da al’ummar duniya da ake tunanin nan da shekarar 2050 za su kai mutum biliyan 10 suka dogara da ita.