An koka da fim din ‘Matar Jami’a’ saboda cin zarafin dalibai mata
daliban jami’a mata sun koka da sabon fim din da aka fitar kwanan nan mai suna ‘Matar Jami’a’ saboda a cewar su fim din ya ci mutuncinsu. daliban sun yi zargin cewa fim din ya alakanta su da cewa sun faye son abin duniya da jiji da kai, kamar kuma yadda suka kasance masu dabi’ar […]


daliban jami’a mata sun koka da sabon fim din da aka fitar kwanan nan mai suna ‘Matar Jami’a’ saboda a cewar su fim din ya ci mutuncinsu. daliban sun yi zargin cewa fim din ya alakanta su da cewa sun faye son abin duniya da jiji da kai, kamar kuma yadda suka kasance masu dabi’ar yaudara da sharholiya.
Fim din dai wanda ya kunshi fitattun ’yan wasa kamar Ali Nuhu da Ibrahim Mandawari da Halima Atete da A’isha Aliyu (Tsamiya) yana ba da labarin iyalai biyu ne, gidan masu ilimi da kudi da kuma gidan talakawa, wadanda kuma ba su yi ilimin zamani ba.
A fim din, an nuno yadda auren Mahmud (Ali Nuhu) da Fadila (Halima Atete) ya lalace, duk da cewa bai dade ba. Ita dai Fadila, ‘yar wani hamshakin dan boko ce, wacce ke karatun jami’a. An nuno yadda ta rika wulakanta aure, yadda ba ta yin biyayya ga mijinta kamar yadda al’ada da addini suka tanada.
Fadila ta mayar da hankalinta kacokan ga karatun boko, wanda haka ya sanya ta yanke kudurin cewa ba za ta yarda ta dauki ciki ba har sai ta kammala karatunta na jami’a. Haka kuma ta kasa hakurewa ta zauna da kishiyar da ba ta yi boko ba, wanda haka ya sanya auren nata ya mutu.
Daga bisani sai Mahmud ya auri wata bazawara (A’isha Tsamiya), wacce karatunta na boko iyakarsa sakandire. Ta zama bazawara ce a sakamakon mutuwa da mijnta ya yi, ya bar ta da da daya. Auren nasu ya gudana cikin fahimta, inda ta rika kyautata wa mijinta, ta rika kula da shi sosai, ba kamar yadda tsohuwar matarsa ta rika wulakanta shi ba. Daga bisani Fadila ta gama karatunta, ta samu aiki amma dai ta kasa samun mijin aure kuma tana ji tana gani tsohon mijinta da matarsa cikin farin ciki da walwala. Wannan ya sanya ta shiga bakin ciki da damuwa.
Mafi yawa daga dalibai mata ’yan jami’a da suka kalli fim din, sun koka da yadda aka wulakanta su kuma aka tozarta su. Sun bayyana cewa an yi musu kazafi, yadda aka nuna akasin yadda rayuwarsu take a zahiri. Sun bayyana cewa yadda fim din ya nuna, yana kashe gwiwar kamfen din da ake na neman diya mata su nemi ilimin zamani.
Kamar yadda Zelfa Ado Zango, wata dalibar Jami’ar Bayero Kano ta ce, fim din ‘Matar Jami’a’ ya ci zarafin daliban jami’a mata. Ta kara da cewa mafi yawan dabi’un da mata suka nuna a fim din ba nakwarai ba ne.
“Idan ka kalli abin da ke faruwa a cikin al’ummarmu, kai har su kansu masu shirya fina-finan na Hausa, musamman matan, ba su da ilimi kuma ba su dadewa a dakin aure. Don haka dabi’ar yarinya ta ta’allaka ne da irin tarbiyyar da ta taso da ita daga gida amma ba wai laifin karatun jami’a ba.” Inji ta.
“Ina ganin ba daidai ba ne a ce za a la’anci fim din, kawai domin ya nuna rayuwar wasu karkatattun dalibai mata na jami’a.” Inji wata dalibar.
Zainab Baba, dalibar da ta kammala Jami’ar Bayero Kano (Sashin Aikin Jarida) ta ce duk da cewa wasu sassan da aka nuna a fim din suna faruwa da gaske, amma dai bai kamata ba da masu shirya fim din suka yi kudin goro wajen lalata sunan daliban jami’a mata.
“Ni na kalli fim din kuma a gaskiya wasu dabi’un da aka nuna a cikinsa suna faruwa a zahiri. Akwai wasu matan aure ne amma sai ka ga suna rayuwa kamar ba matan aure ba. Hasali ma, akwai wata mata da ke saka kaya, sai ka yi tsammanin ita ba macen aure ba ce. Irin yadda za ka ga tana hulda da dalibai maza ’yan ajinsu, za ka ga
cewa abin bai dace ba.” Inji Zainab.
Amma ta ce duk da haka, akwai matan jami’a masu kamun kai da ladabi da biyayya. Za ka ga suna nuna dabi’a mai kyau, yadda ko magana za su yi da malami, sai in ta kama dole.
Shi kuwa furodusan fim din, Muhammad Auwal, a zantawarsa da wakilinmu, ya ce shi ba ya shirya fim din domin cin zarafin dalibai mata na jami’a ba. “Dalilin da ya sanya muka shirya fim din, domin mu nuna wasu daga cikin munanan dabi’un da ke faruwa ne a al’ummarmu domin a gyara.”
Furodusan ya kara a cewa: “Dukkanmu za mu iya yin kuskure, kuma a shirye muke mu amshi gyara domin ta haka ne za mu iya inganta ayyukanmu.”