An koka da halayen wasu shugabannin Fulani a Zamfara

Shugaban masu aikin sa-kai da ke farautar barayin shanu a kasar nan, Alhaji Shehu Musa Aljan ya koka da halayyar wasu shugabannin Fulani da ya yi zargin suna taimaka wa barayin shanu da ake fama da su a kasar nan. Alhaji Shehu Aljan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai […]

An koka da halayen wasu shugabannin Fulani a Zamfara
An koka da halayen wasu shugabannin Fulani a Zamfara

Shugaban masu aikin sa-kai da ke farautar barayin shanu a kasar nan, Alhaji Shehu Musa Aljan ya koka da halayyar wasu shugabannin Fulani da ya yi zargin suna taimaka wa barayin shanu da ake fama da su a kasar nan.

Alhaji Shehu Aljan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Funtuwa, bayan ya samu nasarar kwato daruruwan shanu daga barayi a makon jiya.
Ya kara da cewa bayan shugabannin Fulani ba su iya kwato wa Fulani makiyaya hakkokinsu, sai ya zama da wasu daga cikinsu ake hada baki ana yi wa Fulanin fashi.
Mafaraucin dai ya shiga cikin dazukan kewayen Katsina ne, inda ya samu nasarar kwato daruruwan shanu da tumaki daga wajen wadanda ake zargin kuma ya kawo su Funtuwa ga jami’an tsaro. Ya ce yana rokon barayin da su daina wannan muguwar sana’a haka kuma masu taimaka musu suna hada baki da su, su ma su daina.
Domin a cewarsa, wannan gwamnati, gwamnati ce mai yaki da ’yan ta’adda kuma ba za ta rungume hannu tana kallonsu suna kuntata wa jama’a suna cin karensu babu babbaka ba.