An Kona Gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Anambara
’Yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun cinnna wa gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Anambra, Pacal Agbodike wuta. Baya ga mataimakin shugaban majalisar, an cinna wa gidan wani basarake wuta, da wasu gine-gine mallakin shugabannin wani kauye da ke mazabar Anambra ta Kudu. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 8 […]
’Yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun cinnna wa gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Anambra, Pacal Agbodike wuta.
Baya ga mataimakin shugaban majalisar, an cinna wa gidan wani basarake wuta, da wasu gine-gine mallakin shugabannin wani kauye da ke mazabar Anambra ta Kudu.
Wanna lamari dai ya sanya masu ruwa da tsaki a mazabar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) yin taron gaggawa a jihar kan batutuwan da suka shafi wayar da kan masu zabe, da kuma halin da tsaro ke ciki a jihar.
Kazalika a taron Kwamishinar Zabe ta jihar, Queen Elizabeth Agwu ta ce lokaci ya yi da ya kamata matasan Anambra su farka, domin masu jefa yankin cikin wannan yanayi ba baki ba ne, mutanen yankin ne.
“Dole ne mu gudanar da zaben 2023 a yankin nan namu, kuma dole ne ya zama mai inganci kuma mara magudi.
“Wannan ne lokacin da ya kamata matasa su tashi tsaye don kare mutanensu daga wannan masifa.
“Mun kammala shirin shiga zabe da kayan aiki, abin da muke bukata daga al’umma kawai shi ne karbar katin zabensu na dindindin.
“Duk wani abu da za a yi da zai kawo cikas ga gudanar da zabe a Anambra ta Kudu mu yi masa turjiya, kuma duk wanda aka kama yana yin abubuwan da ba su kamata ba, a dau matakin da ya dace a kansa,” in ji ta.