An kona gidan mawakin siyasa Rarara a Kano

Wasu da ake zargi ’yan daba ne sun banka wa gidan fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarada, wuta a Kano.

An kona gidan mawakin siyasa Rarara a Kano

Wasu da ake zargi ’yan daba ne sun banka wa gidan fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarada, wuta a Kano.

Wani makwabcin Rarara ya shaida wa Aminiya cewa jami’an tsaro sun kai dauki wajen fatattakar bata-garin da suka cinna wa gidan.

Sai dai ya bayyana cewa, a yayin da gidan da ke tikin Gidan Zoo, yake ci gaba da ci da wuta, jami’an kashe gobara ba su kai ga isa wurin ba.

Ya kara da cewa an ji karar fashewar abubuwa a cikin gidan, wanda ke iya kasancewa tukunyar gas.

Hakan kuwa na zuwa ne kasa da awa guda bayan Hukumar Zabe ta Kasa ta sanar da Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga da zimmar dakile sabo doka da oda.

Rarara shahararren mawakin siyasa ne musamman ma a Arewacin Najeriya.

Dauda Rarara ya koma yi wa jam’iyyar APC waka tun a shekarar 2015 zuwa yanzu, innda ke yin zambo da habaici cikin wakokinsa.

Wanda hakan ke bakanta ran magoya bayan wadanda aka yi wa zambon

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya