An kona malama don ta ki aure a Pakistan
Wata malamar makaranta ta mutu bayan da wasu mutane suka cinna mata wuta saboda ta ki yarda da baikon da aka yi mata a kasar Pakistan.Iyalan matar mai suna Maria Sadakat, mai kimanin shekara 20, sun ce mutanen sun kai mata hari ne bayan da ta ki yarda da baikon da aka yi mata.‘Yan sanda […]
Wata malamar makaranta ta mutu bayan da wasu mutane suka cinna mata wuta saboda ta ki yarda da baikon da aka yi mata a kasar Pakistan.
Iyalan matar mai suna Maria Sadakat, mai kimanin shekara 20, sun ce mutanen sun kai mata hari ne bayan da ta ki yarda da baikon da aka yi mata.
‘Yan sanda sun ce wasu mutane ne suka shiga gidanta suka yi mata duka kana suka watsa mata man fetur kafin daga bisani suka cinna mata wuta.
Masu fafutuka sun ce hare-haren da ake kai wa matan da suke kin yarda da baikon da ake yi musu ya zama ruwan dare a kasar, kamar yadda BBC ta bayyana.
Akalla mata dubu daya da 100 ne aka kashe a bara a Pakistan, kamar yadda wata kungiyar kare hakkin dan Adam da ke kasar ta bayyana.
Rundunar ’yan sandan kasar ta ce a farkon wannan shekarar wasu mutane a wani kauye sun ba da umarnin a kashe wata yarinya saboda ta taimaka wa wata yarinya ta tsere da saurayinta.