An kona matar aure da ranta kan zargin satar yara a Kaduna

Bayan da aka kai ta ofishin ’yan sanda, taron jama’ar ya bi ta can, suka tilasta wa ’yan sanda sakin ta sannan suka kona ta,” in ji shi.

An kona matar aure da ranta kan zargin satar yara a Kaduna

Wasu fusatattun matasa sun yi wata wata matar aure kisan gilla inda suka suka kona ta da ranta bayan sun yi mata dirar mikiya a hannun ’yan sanda. 

Wannan mummunan lamari ya faru ne bayan an baza ji-ta-ji-tar zargin matar da satar yara a garin Maraban Jos da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Lamarin, wanda ya haifar da tashin hankali, an ce ya samo asali ne daga damuwar da mazauna yankin ke yi kan zargin yawaitar satar yara a yankin.

Aminiya ta tattaro cewa matar tana kan hanyarta ta zuwa wani taron wa’azin addini ne lokacin da wasu matasa suka zarge ta da yunkurin satar yara.

Shaidu sun ce zargin ya bazu cikin gaggawa a cikin al’umma, lamarin da ya jawo taron jama’a masu yawa waɗanda suka kai wa matar hari tare da dukan ta kafin jami’an tsaro su kai dauki.

Daga nan ne aka kai ta wani ofishin ’yan sanda da ke kusa domin ba ta kariya tare da gudanar da bincike.

Sai dai daga baya lamarin ya tabarbare, inda daruruwan matasa suka mamaye ofishin ’yan sandan suna neman a mika musu ita.

Mazauna yankin sun ce mutanen sun fusata ne saboda abin da suka bayyana a matsayin yawaitar rahotannin bacewar yara a yankin, kuma sun ki watsewa duk da kokarin jami’an tsaro na kwantar musu da hankali.

Daga karshe, taron jama’ar ya rinjayi jami’an tsaro, suka kwace matar daga hannun ’yan sanda tare da banka mata wuta da ranta.

Majiyoyi sun ce ’‘yan sanda sun harba bindiga sama domin gargadi da kokarin dakile harin tare da dawo da doka da oda, inda a garin haka aka harbi wani, wasu da dama suka samu raunuka.

Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu ya bayyana matukar kaduwarsa kan lamarin, yana mai cewa matar tana kan hanyarta ne ta zuwa makarantar addini lokacin da aka zarge ta.

“Abin takaici ne yadda zargi kawai zai kai ga irin wannan mummunan sakamako. Matar aure ce mai yara kuma ana cewa tana tafiya ne zuwa karatun addini lokacin da aka zarge ta.

“Ko bayan da aka kai ta ofishin ’yan sanda, taron jama’ar ya bi ta can, suka tilasta wa ’yan sanda sakin ta sannan suka kona ta,” in ji shi.

Ya kara da cewa gawar matar tana nan a wurin lokacin da ya isa da misalin karfe 1:00 na rana.

“Wannan lamari ne da ya kamata ’yan sanda su bincika. Maimakon haka, mutane sun dauki doka a hannunsu,” in ji shi.

Sai dai wani matashi a yankin ya ce mazauna yankin sun fara nuna damuwa sosai kan zargin yawaitar satar yara, abin da ya kara haddasa fushi da zargi a tsakanin jama’a.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce an kai wa matar harin ne bisa abin da ya kira “zarge-zargen karya na satar yara.”

A cewarsa, Jami’in ’Yan Sandan Yankin Maraban Jos (DPO) ya samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:00 na safe cewa ana kai wa wata mata hari bisa zargin satar yara ba tare da wata hujja da ke tabbatar da hakan ba.

“DPO ya jagoranci jami’ansa zuwa wurin cikin gaggawa, ya ceto ta sannan ya kai ta ofishin ’yan sanda domin kariya da bincike. Duk da haka, daga baya daruruwan mutane suka mamaye ofishin ’yan sandan, suka rinjayi jami’an da ke bakin aiki, suka kwace matar, suka kashe ta sannan suka kona gawarta,” in ji Hassan.

’Yan sanda sun bayyana lamarin a matsayin “ta’asa, laifi kuma hari kai tsaye ga doka da oda,” suna masu jaddada cewa babu wani mutum ko kungiya da ke da ikon daukar doka a hannunsa.

Hassan ya bayyana cewa an riga an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin, yayin da ake ci gaba da farautar sauran wadanda ake nema ruwa a jallo.

“An fara cikakken bincike kan lamarin, kuma duk wadanda aka samu da laifi za su fuskanci hukuncin doka,” in ji shi.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, shi ma ya gargadi cewa rundunar ba za ta lamunci daukar doka a hannu ko kai hari kan cibiyoyin ’yan sanda da jami’ansu ba.

Ya bukaci mazauna yankin da su rika kai rahoton duk wani mutum ko abu da suke zargi ga hukumomin tsaro tare da barin doka ta bi hanyarta.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami’an tsaro sun tarwatsa taron jama’ar, kuma zaman lafiya na ci gaba da dawowa a yankin.