An kona ofishin zabe na jihar Abiya
Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke karamar hukumar Isiala-Ngwa ta kudu a jihar Abiya, inda katunan kada kuri’a da dama suka kone kurmus. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sanda SP Geoffrey Ogbonna ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai (NAN) hakan a jiya […]
Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke karamar hukumar Isiala-Ngwa ta kudu a jihar Abiya, inda katunan kada kuri’a da dama suka kone kurmus.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sanda SP Geoffrey Ogbonna ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai (NAN) hakan a jiya Lahadi.
Rahotanni na bayyana cewa, wutar ta fara ne daga bandaki zuwa sauran ofisoshin har zuwa dakin da ake adana katunan kada kuri’ar zabe.