An kona rugar Fulani kan garkuwa da mutane
Mahara sun kona wata rugar Fulani bisa zargin garkuwa da mutane a Jihar Ogun.
Mahara sun kona wata rugar Fulani bisa zargin garkuwa da mutane a yankin Iraye da ke Shagamu a Jihar Ogun.
Mazauna yankin sun kai wa rugar hari, inda suka kona gidaje, suka jikkata mutum daya wasu kuma suka tsere zuwa inda ba a sani ba.
Wakilinmu ya gano cewa al’ummar Iraye na zargin Fulani da hannu a satar mutane da ake yi a yankin.
Wani bidiyo ya fita wanda ke zargin wasu Fulani da hannu a sace wani manomi; Bidiyon ya ce hatsaniyar ta barke tsakanin bangarorin ne a yayin yunkurin kubutar da wadanda ake zargin an sace.
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN, reshen Jihar Ogun, Abdulmumin Ibrahim, ya ce, “An kira ni da misalin karfe 9 na dare cewa an kona rugar Fulani a Sagamu saboda zargin satar mutane.
“Mutanen rugar sun tsere amma akwai mutum biyu da ba a gani ba. Ba za a iya cewa suna raye ko sun mutu ba; Amma zan tuntube ka idan na samu cikakken bayani,” kamar yadda ya bayyana.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce, “Lamarin ya faru ne a Iraye inda ake zargin Fulani makiyaya da yin garkuwa da wani manomi a gonarsa.
“Shi ne mutanen suka je suka kona rugar; An ji wa bafulatani daya rauni kuma an kai shi asibiti ana kula da shi,” inji shi.