An kona wani saboda ya saci tukunyar miya a Kalaba
Gungun samari sun bankawa wani matashi wuta bayan sun sassara shi saboda zargin sa da kwacewa wata mata tukunyar miya bayan ta gama miyar abin cin karin kumallon safe a garin Kalaba.Matashin an cafke shi ne lokacin da yake neman hanyar guduwa ta re da abokanansa guda biyu niki-niki dauke da tukunyar makare da soyayyiyar […]
Gungun samari sun bankawa wani matashi wuta bayan sun sassara shi saboda zargin sa da kwacewa wata mata tukunyar miya bayan ta gama miyar abin cin karin kumallon safe a garin Kalaba.
Matashin an cafke shi ne lokacin da yake neman hanyar guduwa ta re da abokanansa guda biyu niki-niki dauke da tukunyar makare da soyayyiyar miyar.
Majiyar Aminiya, wadda taki bayyana sunan matar da aka yiwa satar miyar da kuma matashin da aka kona ta ce abin dai kamar da karar kwana domin ana zatan kanshin miyar ne ya ja hankalin matashin da abokanan nasa har suaka shiga gidan matar da yake kusa da cocin katolika ta St Bernard dake Mayne Abenue Edtension a kudancin kalaba.
Wani daga cikin wadanda suka ga yadda abinda ya faru sun ce “ana zargin cewa yaran sune suke yin dauke-daude da sace-sace a unguwar”.