An kone gidaje a artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan IPOB a Imo
Ana fargabar mutane da dama sun mutu sannan an kone dukiyoyi masu yawa bayan wata taho-mu-gama da aka yi tsakanin ’yan IPOB da jami’an tsaro.
Wane sashe na kasuwar Orlu da aka kona a sakamon tarzomar
Ana fargabar mutane da dama sun mutu sannan an kone dukiyoyi masu yawa bayan dauki ba dadin da aka yi tsakanin ’yan Tawayen Fafutukar Kafa Kasar Biafra ta IPOB da jami’an tsaro.
Lamarin dai ya faru ne a garin Orlu na Jihar Imo, sakamakon wani rikici ya samo asali a makon jiya inda aka ba hammata iska tsakanin ’yan kungiyar da jami’an sojoji da na ’yan sanda.

Wasu rahotannin sun kuma ce a sakamakon harin, an sami rasa ran wasu daga cikin jami’an tsaron.

Sai dai suma yanzu haka an ce suna nan sun kuduri aniyar daukar fansa a kan ’yan tawayen.