An kone mutane da ransu a ofishin NNPP a Kano

An cinna musu wuta a wani ofishin Jama’iyyyar NNPP da ke Karama Hukumar Tudun Wada a Jihar Kano

An kone mutane da ransu a ofishin NNPP a Kano

Ofishin ‘yan sandan da aka kona a Neja. (Tsohuwa ajiya).

Mutum uku sun mutu bayan an cinna musu wuta a wani ofishin Jama’iyyyar NNPP da ke Karama Hukumar Tudun Wada a Jihar Kano.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce wasu ’yan daba ne suka kai hari a ofishin jam’iyyar suka cinna masa wuta, sannan an kai makamancin harin a ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na karamar hukumar.

Ya ce, “An kona wasu mutum biyu  da ransu a cikin wata mota a ofishin yakin neman zaben dan takarar Majalsiar Tarayya na Jam’iyyar NNPP.

“Dandazon wasu ’yan daba kuma sun yi yunkurin kona ofishin INEC na Karamar Hukumar Tudun Wada a lokacin da ake tsaka da tattara sakamakon zabe.”

Ya ce a ranar Lahadin da hakan ta faru, wasu ’yan daba sun tayar da rikici tare da yunkurin kona ofishin INEC na Karamar Hukumar Takai, a lokacin da ake tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ’yan Majalisar Tarayya.

Sai dai Kiyawa ya ce jami’an tsaro sun kai dauki cikin gaggawa inda suka tarwatsa matasan suka cafke hudu daga cikinsu.

“Daga baya matasan suka taru suka tare hanyar zuwa ofishin INEC din, amma jami’n tsaro suka sake zuwa suka fasa su.

“An garzaya da mutum daya da ya samu rauni a cikinsu zuwa asibiti, inda likitoci suka sanar cewa ya rasu, sauran hudun ana tsare da su.”

Ya ce jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin gurfanar da wadanda ake zargin don su fuskanci hukunci.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

Tags