An kone ofishin ‘yan sintiri na garin Kafanchan
A daren Juma’ar makon da ya gabata ne da misalin karfe biyu na dare wasu da ba a kai ga tantance ko su waye ba suka sa wa ofishin ’yan sintiri na bijilenti, reshen karamar Hukumar Jama’a da ke Kafanchan cikin Jihar Kaduna wuta, inda ya kone dukkanin takardu da sauran kayayyakin da ke cikin […]

A daren Juma’ar makon da ya gabata ne da misalin karfe biyu na dare wasu da ba a kai ga tantance ko su waye ba suka sa wa ofishin ’yan sintiri na bijilenti, reshen karamar Hukumar Jama’a da ke Kafanchan cikin Jihar Kaduna wuta, inda ya kone dukkanin takardu da sauran kayayyakin da ke cikin ofisoshin guda biyu da hade da juna.
Mataimakin Kwamandan rundunar na karamar Hukumar Jama’a Yahaya Usman Rahama ya shaida wa Aminiya cewa wannan lamarin yana da matukar daure kai, duk da yake ta wata mahangar, za su iya cewa kokarin da suke yi ne wajen sanya ido kan wasu batagari.
Ya bayyana wa Aminiya cewa da misalin karfe biyu abin ya faru, inda bata garin suka yi amfani da soson kujeru masu laushi da ke harabar ofishin da kuma bencinan da ke waje su a tuttura su ta tagogin ofishin da suka farfasa sannan suka cilla wuta a ciki.
Shugaban ya kuma kara da cewa su dai a halin yanzu babu wani ko wasu da suke zargi amma suna fatan Allah Ya tona asirinsu, inda a karshe ya yi kira ga hukumomi da sauran masu hannu da shuni da su taimaka da wajen gyara musu ofisoshin don samun damar ci gaba da aikin taimakon al’umma da su ka sanya a gaba.