An kone ’yan ta’addan da suka kashe malamin makaranta

A cikin daren Laraba wayewar garin Alhamis ne mutanen garin Tudun Saibu a karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna suka kwana suna yin artabu da wasu da ake zaton ’yan fashi inda suka kashe wani magidanci mai suna Halliru Murtala Ciroma mai kimanin shekara 55 da ke zaune a Layin Shakamaki Tudun Saibu.Wadanda ake zargi […]

An kone ’yan ta’addan da suka kashe malamin makaranta
An kone ’yan ta’addan da suka kashe malamin makaranta

A cikin daren Laraba wayewar garin Alhamis ne mutanen garin Tudun Saibu a karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna suka kwana suna yin artabu da wasu da ake zaton ’yan fashi inda suka kashe wani magidanci mai suna Halliru Murtala Ciroma mai kimanin shekara 55 da ke zaune a Layin Shakamaki Tudun Saibu.
Wadanda ake zargi da kashe Malam Halliru Ciroma akwai dan uwansa mai suna Abdullahi da abokansa da wasu makwabtan unguwa da ya gayyato domin su yi wa dan uwansu fashi.
Aminiya ta ziyarci garin Tudun Saibu, inda ta tarar da mutane cikin damuwa tare da kuka ganin irin wannan tashin hankali da suka samu kansu a ciki na kisan gilla da cin amana da ya faru a garinsu, wanda hakan ya sa su cikin dimuwa.
Wakilinmu ya ji ta bakin uwargidan marigayin mai suna Habiba Halliru da suke tare shekara 25, inda ta ce: “A ranar Laraba da misalin karfe 1:00 na dare mutanen suka shigo gidanmu suka tarar da maigidana suka fara dukansa da sanduna da kuma sararsa da adda, suka ce ina kudin da ya karbo a banki? Ya ce layi ya yi yawa bai samu ya karba ba, don haka ba kudi a hannunsa. Hayaniya da bugun da suke yi masa sai matansa mu hudu muka fito gaba dayanmu a rude suna duka suna sara suka ce mu nuna musu inda ya ajiye kudi. Muka ce ai ba ya da kudi a gida daga nan shi maigidanmu ya fara ihu barayi. Suka ci gaba da sararsa, suka ce ya daina ihu. Dama wadannan barayi kusan duk an san su, domin dayansu dan gida ne ba dakin da ba ya shiga a gidan nan. Kasancewar an gane su domin maigidanmu ya ce har da kai Abdullahi? To daga nan ne fa hankalinsu ya tashi suka ci gaba da sara ba ji ba gani, dayansu ya kawo min sara da adda sai na haura ta katanga na dira makwabta.”
Habiba ta kara da cewa daya daga cikin ’yan fashin ya sa kaya irin na sojoji kuma fari ne yana da bille kuma yana dauke da bindiga wadda da ita ce suka harbi maigidansu a cinya. Ta ce wannan mai kayan soja mai bille tana  zaton bako ne.
Ta ce ana cikina haka ne sai mutane da dama suka bullo ta ko’ina don kawo dauki, sai ’yan fashin suka haura suka bar maigidansu a cikin jini. Ta ce lokacin da jama’a suka ga halin da yake ciki ne sai suka yi kokarin kai asibiti, amma kafin su isa rai ya yi halinsa.
Habiba Halliru ta ce “A lokacin da suke sararsa sai muka ce ku yi hakuri kun ga yana da yara kanana, amma sai suka ce me ya dame mu da yaranku.”
Ta ce da  jama’ar gari suka kewaye unguwar gaba daya sai aka shiga farautar wadanda suka yi wannan mugun aiki, tunda dama an san wasu. Ta ce akwai Iroro, akwai Usman da Abdullahi dan uwan marigayi mijinsu.
dan uwan marigayin mai suna Abdulahi wanda ya shaida wa wakilinmu ce=wa an buga masa waya da daddare cewar ga abin da yake faruwa, ya ce daga nan ya nufo gidan ya ga abin da ya faru sai ya yi ta kokarin kula da dan uwansu sauran mutane suna ta kokarin nemo ’yan fashin suka buya, kuma ana kama daya daga cikinsu mai suna Iroro Boss sai ya fara bayyana wadanda suka yi wannan aika-aika. Ya ce da Ado Fakasu da kuma Abdullahi Bagi da kuma wani wai shi Lawal Awai, sannan ya fadi wadansu mutum biyu a Soba. Ya ce ank amo Abdullahi Fakasu domin a ci gaba da yi musu tambayoyi sai su kuma mutanen gari suka fusata inda suka far musu suka sassare su suka sanya musu wuta suka kone su.
Ya kara da cewa, “Shi kuma dan uwan namu mai  suna Abdullahi Bagi bai dauka cewa asiri ya tonu cewa da shi a ciki ba. Don haka ya tafi makabarta domin hakar kabarin dan uwanmu, to a can ne jama’a suka far masa shi ma suka kashe shi suka kone. Shi kuma Lawal Awai wanda shi ne aka ce yana da bindiga a cikinsu, dama kowa ya san shi dubunsa ce kawai ba ta cika ba, sai a wannan karo, an ce kayan mata ya sa ya rufe jikinsa ya gudu ya bar garin. Kuma mun samu labarin cewa an kama wasu mutum biyu a garinsu an tafi da su. Yaran nan uku da aka kashe dukkansu makwabta ne makon da ya wuce ma sai da suka zo wurin marigayi suka ce sun tuba ba za su sake yin abin da suke yi ba ya dauki Naira dubu 15 ya ba su ya ce musu kowa ya je ya yi tunanin irin sana’ar da zai iya yi su dawo su fada masa domin ya ba su jari, amma ba a kai ko’ina ba a cikin wannan mako suka kashe shi.”
Hakimin Maigana Alhaji Muhammadu Buhari wanda ya yaba halin marigayin, ya ce mutum ne mai tausayi da son taimaka wa al’umma. Don haka duk da ya taba rike mukamin kansila sau biyu hakan bai sa shi ya daina zuwa karantarwa ba a makaranta domin malami ne wanda yake koyar da lissafi a makarantar sakandare. Ya ce kuma a harkar kasuwanci ba baya ba ne domin yana daya daga cikin masu harkar sayarda amfanin gona a kasuwar Tudun Saibu. “Don haka ka ga jama’a ta ko’ina suna ta bullowa domin ta’aziyya,” inji Hakimin.
Ya kara da cewa irin matakan da suke dauka na tsaro dama can sun san da irin wadannan hatsabiban yara domin duk sunayensu na wurin jami’an tsaro ana ana sa ido a kansu. Kuma ya yi kira ga iyayen yara su rika sa idanu ga ’ya’yansu.     
Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta daya da ke Zariya, Muhammad D. Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce saboda sanin wadanda suka aikata abin ne mutanen gari suka kashe mutum uku tare da kone gawarwakinsu. Kuma mun kama mutum biyu wasu kuma daga cikinsu sun tsere, “Kuma muna nan mun sa ido domin kamo duk wanda yake da hannu a cikin kashe wannan malami, kuma muna ba da kulawa a yankin domin natsuwa ta dawo jikin al’ummar garin,” inji shi.