An kori dalibai 175 a Jami’ar Jihar Kwara
Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) ta kori dalibai 175 a lokaci guda
Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) ta kori mutum 175 daga cikin dalibanta kan aikata wasu laifuka daban-daban.
Kakakin Jami’ar KWASU, Dr. Saeedat Aliyu, ta sanar cewa laifukan da aka kori daliban a kansu sun hada da satar jarabawa, zamba, sace-sace, shiga kungiyoyi marasa rajista, amfani da takardun bogi, mallamar makami ba bisa ka’ida ba da kuma tayar da rikici.
Dr. Saeedat Aliyu ta kara da cewa an amince da korar daliban ne bayan karbar rahoton kwamitin ladabtarwan jami’ar da ya binciki abubwan da suka faru daga watan Oktoban shekarar 2021 zuwa watan Maris na 2024.
“Hukumar gudanarwar Jami’ar KWASU na jaddada cewa ba za ta lamunci kowane nau’in rashin da’a ba kuma za ta ci gaba da yin tsayuwar daka wajen ba da ilimi da kyawawan dabi’u,” in ji sanarwa.