An kori dan kwallo bayan mintoci da sanya hannu a kwantaragi

Wani abu mai kama da almara ya faru a Sifen a karshen makon jiya bayan da kulob din Deportibo La Coruna da ke buga wasa a gasar rukuni-rukuni na Sifen ya kori wani dan kwallo mai suna Julio Rey jim kadan bayan ya rattaba hannu a kulob din. Kulob din ya ce dalilin da ya […]

An kori dan kwallo bayan mintoci da sanya hannu a kwantaragi
An kori dan kwallo bayan mintoci da sanya hannu a kwantaragi

Wani abu mai kama da almara ya faru a Sifen a karshen makon jiya bayan da kulob din Deportibo La Coruna da ke buga wasa a gasar rukuni-rukuni na Sifen ya kori wani dan kwallo mai suna Julio Rey jim kadan bayan ya rattaba hannu a kulob din.

Kulob din ya ce dalilin da ya sa ya kori dan kwallon shi ne yadda ya taba aika sakonnin batunci ga kulob din a kafar sadar da zumuntarsa na twitter a shekarun baya.
Kulob din ya ce kimanin shekaru uku da suka gabata ne dan kwallon a lokacin yana kwallo a wani kulob ya rika yin kalamun batunci ga kulob din ba tare da wata kwakkwarar hujja ba al’amarin da ya sa mahukunta kulob din suka ajiye sakonnin a taskarsu a matsayin hujja.
Duk da yake tuni dan kwallon ya yi nadamar abin da ya aikata inda tuni ya goge sakon daga kafar sadarwar tasa amma yin hakan bai sa kulob din ya yafe masa ba. Abin takaicin shi ne sai bayan da kulob din Deportibo ya watsa hotunan dan kwallon a kafar sadarwarsa na yarjejeniyar da suka kulla ne sannan ya gano ashe shi ne dan kwallon da ya rika muzanta su, al’amarin da ya sa mahukunta kulob din suka yi taron gaggawa inda suka yanke shawarar sallamarsa a kasa da awa daya da sanya wa kulob din hannu.
Tuni dai dan kwallon ya tattara nasa-ya-nasa ya bar kulob din. Duk kokarin da manema labarai suka yi na tuntubar dan kwallon a kan batun ya ci tura.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja