An kori dan sandan da ya kashe wani mutum daga aiki
An sallami shi daga aiki bayan gano ya kashe mai babur din da gangan.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun ta sanar da korar wani jami’inta daga aiki saboda ya kashe wani mutum a kan babur a garin Osogbo.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa dan sandan ya harbe mutumin mai suna Saheed Olabomi ne ranar 27 ga watan Yuli.
– Cutar COVID-19 ta kashe mutum 11 a Najeriya
– Yajin aiki: Gwamnatin Tarayya ta maka likitoci a kotu
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, SP Yemisi Opalola, ya fitar a ranar Juma’a game da sallamar dan sandan.
“Kamar yadda Kwamishinan ’Yan Sanda Olawale Olokode ya yi alkawari za a bayyana sakamakon shari’ar …an yi wa F/NO.467549 Sajan Adamu Garba shari’a bisa Dokokin Aikin Dan Sanda na Najeriya.
“An sami dan sandan da aikata laifin da aka zarge shi da aikatawa kuma an kore shi daga aiki.
“An tura wa Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Abuja hukuncin shari’ar domin daukar matakin gurfanar da shi a gaban kotu.
“Kwamishina ya jinjina wa jama’ar jihar nan saboda bin doka tare da kauce wa daukar doka a hannu, wanda hakan ya ba da damar yin bincike yadda ya kamata.”
Kwamishinan ya ja hankalin jama’ar jihar da su ci gaba da kasancewa masu bin doka a kodayaushe don tabbatar da hukuncin da ya dace a kan kowane lamari.