An kori gawar dan sanda daga aiki
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kori gawar wani dan sanda mai mukamin Sufeto daga aiki, bayan da ya kashe wani ma’aikacin Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASMAN) lokacin da ya hana shi keta dokar bin hanya. Dan sandan mai suna Sufeto Olakunle Olanade da ke aiki da ayarin ’yan sanda […]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kori gawar wani dan sanda mai mukamin Sufeto daga aiki, bayan da ya kashe wani ma’aikacin Hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASMAN) lokacin da ya hana shi keta dokar bin hanya. Dan sandan mai suna Sufeto Olakunle Olanade da ke aiki da ayarin ’yan sanda na FSARS a ofishinsu na Ikeja a Legas ya harbe wani jami’in Hukumar LASMAN ne a ranar Larabar makon jiya, lokacin da jami’in mai suna Adeyemo Rotimi ya yi kokarin hana shi biyowa ta hannu da ba nasa ba a yankin Yanapaja, inda ya tsayar da shi, amma nan take cikin fushi dan sandan ya fito da karamar bindiga ya bindige shi.
Nan take matasa suka rufar wa dan sandan lokacin da ya yi shirin gudu, suka cim masa suka yi masa dukan kawo wuka, kafin wadansu ’yan sanda su kwace shi su garzaya da shi asibiti, inda ya rasu a kan hanya.
Wata sanarwa da Kakakin ’Yan Sandan Jihar Legas Chita Oti ya fitar a kan lamarin, ta ce hukumar ’yan sandan ta yanke wa gawar dan sandan da ya yi aika-aikar hukunci, inda aka kori Olakunle Olanade daga aiki duk da ya rasu.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Mista Edigal Emohimi ya bayyana takaicinsa bisa aukuwar lamarin.
Babban Daraktan Hukumar LASMAN, Musa Oluwale ya ce mafi yawan masu keta dokar hanya a lokacin da suke tuki a birnin Legas jami’an tsaro ne masu kayan sarki, ya ce sau tari jami’an tsaron da suka hada da ’yan sanda da soji kan ci zarafin jami’an nasu da ke aiki dare domin magance cinkoson ababen hawa a birnin Legas.