An kori gwagware 600 daga gidan haya a Abu Dhabi
Hukumar Kula da Birane ta kori gwagware 600 daga wasu gidajen alfarma, inda daya daga cikin gidajen mai hawa shida da ke dauke da dimbin jama’a a kan titin Hamdan da ke birnin Abu Dhabi ta Hadaddiyar Daular Larabawa. Gidan da ke tsakanin titunan Hamdan da Electra, yana karkashin kulawar masu gidan, ba tare da […]
Hukumar Kula da Birane ta kori gwagware 600 daga wasu gidajen alfarma, inda daya daga cikin gidajen mai hawa shida da ke dauke da dimbin jama’a a kan titin Hamdan da ke birnin Abu Dhabi ta Hadaddiyar Daular Larabawa. Gidan da ke tsakanin titunan Hamdan da Electra, yana karkashin kulawar masu gidan, ba tare da wakilci ba.
A cewar daya daga cikin mazaunan gidan, mun samu takardar korarmu daga gidan ne, daga hannun Hukuma Kula da Birnin, kimanin mako guda da ya wuce. “Kimanin mu takwas da ke zaune a wani gida, muna biyan Dirhami dubu biyu da 500 (Naira dubu 100) a kowane wata,” inji Mohammed Ala, dan asalin kasar Bangaladesh.
Sashen fitar da ’yan haya da ke karkashin hukumar birni, ya taba sallamar gwagware dubu daga gidajensu. A cewar hukumar da wakilin mai gidan, a cika gidan fiye da kima, “ kuma irin wannan al’amari, “yana munana darajar birnin, sannan ya haifar matsalolin kula da lafiya.”
Su kuwa gwagwaren da ke haya a gidan Freej Al Sayegh, tuni suka fara neman dan wurin da za su sanya gadajen kwanciyarsu a makwafta.
“Muna fatan samun wurin da za mu hada karfi mu kama dakuna. Tunda ayyukan da muke yi ba za su ba mu damar zama a Musaffah ko Baniya, kuma harkokin neman abincinmu na cikin birni ne, don haka muke bukatar samun wani sabon wurin,” inji Abdul Rahman Kutty.
Shi ma wani Ba’indiye da ya fito daga Hyderabad, ya yi bayani kan yadda hukumar birnin ta kai karar ’yan haya, inda ake tuhumarsu da ka’idojin hayar, ta hanyar sake bayar da hayar gidajen da suka karba, al’amarin da ya haifar da cunkoso a gidajen hayar. Ita dai dokar haya a Abu Dhabi ba a wuce mutum uku a daki guda.