An kori hafsohin ’yan sanda 19 daga aiki
An kori hafsoshin ’yan sandan Nijeriya 19 daga aiki, an rage wa wani mataimakin Kwamishina da wasu 18 matsayi, bayan kama su da aikata laifi a bakin aiki
Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta kori mayan hafsoshin ’yan sanda 19 tare da rage wa wasu 19 mukami a ranar Juma’a.
Shugaban hukumar, AIG Haruna (murabu), ya ce, An yanke wa ’yan sandan hukuncin ne bayan samun da laifuka daban-daban da aka bincinke su a kai bayan an zarge su a aikatawa.
Wadanda aka kora sun hada da masu mukamin ASP guda 10 da DSP guda shid sai CSP guda biyu dakuma SP daya.
Ya bayyana cewa hukumar ta ba da takardar gargadi mai tsauri ga wani Mataimakin Babban Hafsan Dan Sanda kan rashin bin umarnin gudanar da aiki.
- Jami’an tsaro sun hana Sarkin Kano fitowa daga fadarsa
- Karin aure: Maza ku yi adalci, mata ku daina tsoro —Malamai
- Muhammad ne sunan da aka fi sa wa yara maza a Ingila
Sanarwar da kakakin hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce sauran hafsoshin ’yan sandan da aka rage wa matsayi sun kunshi Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda daya da CSP daya da SP biyu da DSP biyu da ASP 13.