An kori iyalan dan-ga-ni-kashe-nin Messi daga Afghanistan

Iyalan yaron nan dan kimanin shekara biyar Murtaza wanda ya zama dan-ga-ni-kashe-nin Lionel Messi da ke zaune a Afghanistan tare da mahaifansa sun yi kaura zuwa wata makwabciyar kasa saboda yadda kungiyar ’yan Taliban take yi musu barazana ba dare, ba rana, kamar yadda kafar sadarwar Fodnews ta kalato.Rahoton ya nuna tun bayan da shahararren […]

An kori iyalan dan-ga-ni-kashe-nin Messi daga Afghanistan
An kori iyalan dan-ga-ni-kashe-nin Messi daga Afghanistan

Iyalan yaron nan dan kimanin shekara biyar Murtaza wanda ya zama dan-ga-ni-kashe-nin Lionel Messi da ke zaune a Afghanistan tare da mahaifansa sun yi kaura zuwa wata makwabciyar kasa saboda yadda kungiyar ’yan Taliban take yi musu barazana ba dare, ba rana, kamar yadda kafar sadarwar Fodnews ta kalato.
Rahoton ya nuna tun bayan da shahararren dan kwallon Ajentina Lionel Messi ya aika wa Murtaza rigarsa ta kwallo mai dauke da lamba 10 da kuma wadansu kyaututtuka ne iyalan nasa suka samu kansu a cikin wannan matsala.
Kamar yadda mahaifin yaron mai suna Ahmadi ya nuna a wata hira da ya yi da kafar sadarwar ta Fodnews ya ce “Da farko ban yi niyyar barin Afghanistan ba, amma da na fahimci kullum rayuwarmu tana cikin hadari ta hanyar samun sakonnin da ke yin barazana ga lafiyar dana da ta iyalina ne na yanke shawarar yin kaura bayan na sayar da kadarorina inda yanzu haka muka koma wata makwabciyar kasa”.
“Bayan Messi ya samu labarin dana ne sai ya aiko masa da rigar kwallonsa mai dauke da suna da kuma lamba 10 da kuma wadansu kyaututtuka, to daga nan ne fa yaron da daukacin iyalanmu muka tsinci kanmu a mawuyacin hali inda kullum ake aiko mana da sakonnin barazana ga rayuwarmu”, inji mahaifin yaron.
kungiyar Taliban dai ta rika yi wa iyalan Murtaza barazana ne tun bayan da ya samu kyauta daga Messi inda ta nuna bacin ranta a kan yadda iyalan Murtaza dan kimanin shekara biyar  suka daure masa gindi wajen son kwallon kafa maimakon koya masa karatun Alkur’ani da wadansu littattafan addini.
Shi dai yaro Murtaza, dan kimanin shekara biyar ya yi suna ne tun bayan da aka hango shi yana kwallo a cikin sa’o’insa sanye da rigar leda mai dauke da sunan Lionel Messi da lamba 10 ta Ajantina.  Hakan ta sa ya janyo hankalin duniya ciki har da Hukumar shirya kwallo ta Afghanistan wacce ta yi yunkurin hada yaron da Lionel Messi don su gana.
Duk da ganawar ba ta yiwu ba Messi ya samu damar aika masa da rigar kwallonsa mai dauke da suna da kuma lamba 10 don karfafa masa gwiwa.  Bayan hakan ta faryu ne sai kungiyar Taliban ta nuna adawarta a kan haka inda ta rika aika wa iyalan Murtaza sakonnin barazana.
Idan za a tuna Aminiya ta buga labarin Murtaza mai taken: dan shekara biyar ya zama dan-ga-ni-kashe-nin Messi”.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa