An kori Janar din soja daga aiki kan badakalar miliyan 400
Rundunar Sojin Najeriya ta kori wani Janar dinta bayan ta rage masa matsayi saboda samun sa da laifin zamba. Kotun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kama Manjo Janar Oladipo Otiki da laifi a badakalar Naira Miliyan 400 da ake tuhumar sa. Kotun sojin ta yanke wa janar din wanda shi ne kwamandan Runduna ta […]
Rundunar Sojin Najeriya ta kori wani Janar dinta bayan ta rage masa matsayi saboda samun sa da laifin zamba.
Kotun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kama Manjo Janar Oladipo Otiki da laifi a badakalar Naira Miliyan 400 da ake tuhumar sa.
Kotun sojin ta yanke wa janar din wanda shi ne kwamandan Runduna ta Takwas hukuncin kora daga aiki bayan samun sa da laifin saba ka’idojin aiki da kuma satar kayan gwamnati.
Hukuncin kotun na daren ranar Litinin, ya rage masa matsayi daga Manjo Janar zuwa Birgediya hadi da hukunci mai tsanani kafin ta kore shi.
- Sojoji sun gudu da miliyoyin kudin kwamandansu
- Kotun sojoji ta kori soja daga aiki kan yi wa ‘yar gudun hijira fyade
- Kotu ta samu Oliseh Metuh da laifin karbar Naira miliyan 400
Da yake yanke hukuncin a Hedikwatar Tsaro, Shugaban Sashen Tsara Manufofi na Rundunar Sojin, Laftanar Janar Lamidi Adeosun ya ce an samei Janar Oladipo Otiki da laifukan da ake zarginsa.
A watan Satumbar bara ne dai Rundunar Sojin ta kafa kotun don ta gudanar da shari’a ga Janar Otiki bisa zargin badakalar kudaden da aka zargi sojojin da ke karkashin kulawarsa da yin awon gaba da su.
Kudaden dai da ake takaddama a kansu kamata ya yi su kasance karkashin kulawar Jami’in Kudi na rundunar, sai dai rahotanni sun nuna an karkatar da su lokacin da Janar Otiki yake rike da mukamin kwamandar rundunar.
Rahotanni sun ce lauyan Otikin ya nemi kotun da ta yi wa wanda yake karewa afuwa sakamakon amsa laifukansa tare da dawo da kudaden da ake shari’a kansu tun da farko.