An kori kamfanin Gombawa Motors daga tashar gwamnati bayan goyon bayan Pantami

An umarci kamfanin da ya fice daga harabar tashar cikin sa’o’i 24 bayan karɓar sanarwar.

An kori kamfanin Gombawa Motors daga tashar gwamnati bayan goyon bayan Pantami

Gwamnatin Jihar Gombe ta ba wa kamfanin motocin Sufuri na Gombawa Motors sa’o’i 24 ya fice daga tashar motoci na Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Park.

Wannan mataki na zuwa ne kwana biyu kacal bayan kamfanin ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan jihar na Jam’iyyar PDP a zaben 2027, Farfesa Isa Ali Pantami.

Takarda korar mai ɗauke da kwanan wata 25 ga Yunin 2026, yana dauke da sa hannun Manajan-Daraktan kamfanin Principal Facilities Management Limited, wanda ke kula da Mega Park, wadda mallakar gwamnatin jihar ce.

Sanarwar da aka aike wa kamfanin Gombawa Motors ta umarci kamfanin da ya fice daga harabar tashar cikin sa’o’i 24 bayan karɓar takardar.

Ta bayyana cewa Kwamitin Gudanarwa na Mega Park ya yanke hukuncin ne bisa zargin kamfanin Gombawa da karya ƙa’idojin gudanar da ayyuka a tashar da kuma jawo koke-koke daga sauran masu harkar sufuri.

An kuma aika kwafen takardar zuwa Kamfanin Hanyoyi da Sauran Ababen More Rayuwa na Jihar Gombe (GROCOL), Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da Hukumar Tsaron Sibil Difens ta Najeriya (NSCDC).

Sai dai takardar korar ba ta ambaci goyon bayan da kamfanin ya nuna wa Pantami ko wata alaƙa da siyasa ba.

Maimakon haka, ta ce an ɗauki matakin ne saboda zargin karya dokokin gudanarwa da kuma koke-koken da sauran masu harkar sufuri suka gabatar.

Mahukuntan Mega Park sun dage cewa korar kamfanin ta samo asali ne daga zargin karya ƙa’idojin aiki, ba wai saboda matsayinsa na siyasa ba.

A nasu bangaren shugaban Gombawa Motors, Alhaji Ibrahim Mustapha, ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya, yana mai cewa goyon bayan ya samu amincewar sama da mambobi 4,000 na ƙungiyar a faɗin jihar.

Mustapha ya ce tun bayan ƙaddamar da Mega Park, an riƙa sauya wa masu harkar sufuri wuraren aiki, lamarin da ya haddasa musu asarar kuɗaɗe masu yawa.

Ya ce ƙungiyar ta kashe sama da Naira miliyan 10 wajen gina tantuna, ofisoshi da sauran kayayyakin aiki a ɗaya daga cikin tashoshin da aka ware musu kafin daga bisani a tashe su zuwa wani wuri, abin da ya ƙara musu asarar masu yawa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga Gwamnatin Jihar Gombe kan zargin cewa korar na da alaƙa da goyon bayan da kamfanin ya nuna wa Pantami.