An kori Kwankwaso, an ƙone jar hula a Neja

Yanzu ana ci gaba da sa ido kan abin da zai faru bayan rikici na ci gaba da tsamari a jam’iyyar.

An kori Kwankwaso, an ƙone jar hula a Neja

Wasu magoya bayan Jam’iyyar NNPP a Jihar Neja, sun yi watsi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin jagoran jam’iyyar.

Shugaban tsagin magoya bayan, Dokta Gilbert Agbo ne ya jagoranci zanga-zangar adawa da Kwankwaso a hedikwatar jam’iyyar da ke Minna.

Ya ce Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya na barazana ga cigaban jam’iyyar.

Yayin taron Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Minna, Dokta Agbo ya jaddada cewa dakatar da Kwankwaso da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa ya yi a Legas, zai kawo ƙarshen tasirinsa a jam’iyyar.

Don adawa da Kwankwaso, Dokta Agbo da mutanensa sun ƙone jar hula a hedikwatar jam’iyyar da ke jihar.

Kazalika, ya ce gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, yana da damar gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar saboda rashin bin dokokin jam’iyyar.

Sai dai a martaninsa, jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya a Jihar Neja, Malam Danladi Umar Abdulhamid, ya bayyana shugabancin Dokta Agbo a matsayin haramtacce.

Ya ce zanga-zangar ba ta da alaƙa da jam’iyyar, sai dai don raɗin kansa.

Abdulhamid, ya tabbatar da cewa Rabiu Musa Kwankwaso har yanzu shi ne jagoran jam’iyyar na ƙasa .

Rigimar da ake yi yanzu a NNPP yana haifar da damuwa kan haɗin kan ’ya’yan jami’yyar.

Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar da masu sha’awar siyasar Najeriya na jiran su ga abin da zai faru a nan gaba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos