An kori ma”aikata 1,774 a Kogi
Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana yi wa sakatarorin dindindin na ma’aikatunta takwas ritaya da daraktocinta tare da korar ma’aikata dubu 1,774. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya gano cewa tuni gwamnati ta mikawa ma’aikatan takardun sallamarsu tun watan Disamban da ya gabata. Shugaban ma’aikatan jihar, Misis Deborah Ogunmola da kuma shugaban hukumar ma’aikatan […]

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana yi wa sakatarorin dindindin na ma’aikatunta takwas ritaya da daraktocinta tare da korar ma’aikata dubu 1,774.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya gano cewa tuni gwamnati ta mikawa ma’aikatan takardun sallamarsu tun watan Disamban da ya gabata.
Shugaban ma’aikatan jihar, Misis Deborah Ogunmola da kuma shugaban hukumar ma’aikatan jihar, Mista Ado Shaibu su ne suka sanya hannu a takardun sallamar.