An kori mazauna NEPA kuarters bayan kama mutum 370
daruruwan mazauna Unguwar NEPA kuarters da aka yi musu rusau a ranar Litinin da ta gabata, sun tattara iyalansu sun bar unguwar bayan da jami’an tsaro suka umarce su da yin haka washegari Talata kamar yadda Aminiya ta samu labari a shekaranjiya Laraba.Wannan ya biyo bayan kama mazauna wurin ne su 370 da jami’an tsaron […]
daruruwan mazauna Unguwar NEPA kuarters da aka yi musu rusau a ranar Litinin da ta gabata, sun tattara iyalansu sun bar unguwar bayan da jami’an tsaro suka umarce su da yin haka washegari Talata kamar yadda Aminiya ta samu labari a shekaranjiya Laraba.
Wannan ya biyo bayan kama mazauna wurin ne su 370 da jami’an tsaron suka yi a ranar Litinin daga bisani ma’aikatan sashin kula da gine-gine na hukumar birnin tarayya suka rusa bacocinsu na sana’a da na kwana.
Tuni dai aka fara gurfanar da wasu daga cikinsu a gaban kotu kan zargin laifuffuka daban-daban, a yayin da wasu kuma a ka kai su sashin yaki da fashi da makami (SARS), don ci gaba da bincike. Wasu kuma an ce a tura keyarsu zuwa Jamhuriyar Nijar da ake cewa kasarsu ta asali ce.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Abuja, DSP Hyelhira Altine Daniel wadda ta tabbatar da kama mutanen da gurfanar da wasu a gaban kotu tare da mika wasu ga SARS, sai dai ba ta tabbatar da kai wasu zuwa Nijar ba, inda ta ce jami’an kula da shigi-da-fice ne suka dace su yi bayani a kai. Wata majiya mai tushe a kamfanin wutar lantarki (PHCN), ta tabbatar da cewa gidajen na NEPA kuarters an gina su ne don manya da matsakaitan ma’aikatan tsohuwar Hukumar NEPA, sai dai ta ce an gwanjatar da gidajen, lamarin da ya sa aka yi watsi da su.
Majiyar ta ce gabanin gwanjatarwar hukumar ta ba da rukunin gidajen ga gidauniyarta mai kula da sha’anin fansho da warware basussukan ma’aikata, inda gidauniyar ta shigar da kara a kotu tare da kalubalantar saida gidajen.
Majiyar ta ce kotun ta yanke hukuncin da ya goyi bayan sayar da gidajen, amma sun daukaka kara a kotun ta gaba don kalubalantar hukuncin.
Rushe-rushen da ake yi a sassan Abuja ya biyo bayan samamen da jami’an tsaro suka kai Apo ne inda suka kashe mutum bakwai a wani gida da ba a kammala ba a kwanakin baya.
An ci gaba da rusau din a garin Kubwa na tsawon mako daya kuma a ranar Juma’ar da ta gabata an rusa wata kasuwa a garin Karu da ke Abuja, sannan rusau din ya isa Dutsen Alhaji da ke Yankin Bwari a ranar Litinin da Talata.