An kori minista a Bangladesh kan sukar aikin Hajji
kasar Bangladesh ta kori daya daga cikin manyan ministocinta bayan da ya soki aikin Hajji lamarin da ya jawo zanga-zanga daga kungiyoyin Musulmi da suka ce ya yi ridda kuma suka bada awa 24 a sauke shi.Abdul Latif Siddikue, wanda shi ne Ministan Sadarwa na Bangaladesh yana birnin New York a matsayin dan rakiyar Firayi […]
kasar Bangladesh ta kori daya daga cikin manyan ministocinta bayan da ya soki aikin Hajji lamarin da ya jawo zanga-zanga daga kungiyoyin Musulmi da suka ce ya yi ridda kuma suka bada awa 24 a sauke shi.
Abdul Latif Siddikue, wanda shi ne Ministan Sadarwa na Bangaladesh yana birnin New York a matsayin dan rakiyar Firayi Ministan kasar Sheikh Hasina, ya yi wannan katobara wadda aka watsa a gidajen talabijin din kasarsa.
Siddikue ya ce: “Na gaji da batun aikin Hajji da kungiyar Tablig Jamaat. Mutum miliyan biyu suna zuwa Saudiyya don yin aikin Hajji. Hajji barnar dukiya da bata lokaci ne. Wadanda suke zuwa aikin Hajji ba su da wani alfanu a bangaren aiki. Kuma suna kassara tattalin arziki, suna kashe makudan kudi a kasar waje.”
Kalamin nasa ya jawo zanga-zanga nan take daga magoya bayan kungiyar Hefajat-e-Islam wadda shugabanninta suka ce “ya yi ridda” kuma suka ba gwamnati wa’adin ta sauke shi cikin awa 24.
Wani babban jami’in gwamnatin kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP za a cire Siddikue, to amma bai ce ko hakan yana da alaka da bukatar masu kishin Musuluncin ba.
Jami’in wanda ke aiki a ofishin Firayi Ministan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “An yanke shawaar sauke shi daga mukaminsa. Kuma za a yi hakan ne da zarar Hasina ta dawo gida.”
Ministan wanda ya soki tasirin dan Hasina mai suna Sajeeb Waze Joy a wani gangami a New York, ya kuma soki kungiyar Musulunci ta Tablig Jamaat da miliyoyin magoya bayanta ke gudanar da gangami a wajen babban birnin kasar da mahukunta kasar suka ce shin ne taron Musulmi mafi girma bayan na aiki Hajji.
Ministan ya ce, kimanin Musulmi miliyan biyu da ke taruwa “ba su aikin komai ban da jawo cinkoson ababen hawa a daukacin sassan kasar,” inji Siddikui.
Sai dai kungiyar Tablig Jamaat ba ta ce komai kan wannan batu ba.