An kori rakuma 40 a gasar kyan rakuma saboda magudi a Saudiyya

Ana zargin an yi wa rakuman allurar sauya halitta domin kara musu kyan diri

An kori rakuma 40 a gasar kyan rakuma saboda magudi a Saudiyya

An dakatar da rakuma akalla 40 a gasar kyan rakuma a kasar Saudiyya kan zargin an yi musu sauyin halitta don su kara kyan diri.

Rakuman da aka dakatar a Gasar Rakuma ta Sarki Abdulazizi sun hada wadanda aka yi wa allurar Botox domin kara musu kyan diri da wadanda aka sauya musu halitta ko tayar da komadarsu ta wasu hanyoyi na dan Adam.

Alkalan gasar da ke gudana a birnin Riyadh, za su zabo rakumin da ya mafi kyan diri ne ta hanyar la’akari da fasalin kai, wuya, tozo, tsayuwa da kuma adon rakuman da ke fafata domin lashe gasar Dala miliyan 66.

Sai dai kuma an haramta amfani da allurar Botox da duk wani nau’in tayar da komada ko sauya dirin rakuma a gasar, wadda aka gayyato masu kiwon kyawawan rakuma su zo su fafata.

A wannan karon alkalan gasar sun tsaurara bin diddigi ta hanyar “amfani da manyan fasahohin zamani” don gano rakuman da aka sauya wa halitta, a cewa Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA).

“Hukumar ta tashi hankan domin yakar duk wani nau’in magudi da sauya halitta don kara wa rakuma kyau, masu shirya gasar kuma za su yi tsattsauran hukunci ga wadanda aka kama da laifin” inji rahoton.

Ya bayyana cewa a bana hukumomi sun gano wasu rakuma da masu suka yi kara musu tsayin haci da lebe tare da yin amfani da wasu kwayoyin halitta domin kara musu girma da cikar hantsa.

An kuma bankado rakuman da aka kara wa labbansu da kawunasu girma ta hanyar yi msusu allurar Botox; wadana aka daure sassan jikinsu da roba don kara musu kyan diri; da wadanda aka yi wa amfani da wasu abubuwa don kara musu kyan fuska.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina