An kori Seaman Abbas daga aiki
Kotun Dakarun Sojin Nijeriya ta tabbatar da laifukan da ake tuhumar Seaman Abbas.
Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da korar jami’in sojin ruwan nan mai suna Seaman Abbas Haruna daga aiki.
Sallamar Seaman Abbas daga aiki na zuwa makonni bayan mai ɗakinsa da ta bayyana a cikin wani shiri na gidan Rediyon Human Rights ta fallasa irin uƙubar da yake ciki tsawon shekaru shida.
Sai dai bayan wannan fallasa ta yamutsa hazo, Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya, Janar Christopher Musa da Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle suka ba da umarnin gaggauta gudanar da bincike.
Da yake ƙarin haske kan lamarin a yau Laraba yayin ganawa da manema labarai, Darektan Labaran na Rundunar Sojin Nijeriya, Birgediya-Janar Tukur Gusau, ya ce tuni an kori Seaman Abbas daga aiki.
Birgediya-Janar Gusau ya ce sallamar Seaman Abbas daga aiki na zuwa ne bayan da Babban Hafsan Sojin Ruwa na Nijeriya, Emmanuel Ogalla ya amince da hukuncin da Kotun Dakarun Sojin Nijeriya ta yanke kan jami’in sojin a ranar 19 ga watan Satumban bana.
A cewarsa, an gurfanar da Seaman Abbas a gaban kotun ce kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa bijire wa umarni, ƙin bari a kama shi da kuma lalata dukiyar rundunar soji.
Ya ce duk laifukan da aka tabbatar wa Seaman Abbas sun saɓa wa sashe na 56 da 86 da kuma na 66 na Kundin Dokokin Rundunar Sojin Nijeriya na 2004.
Birgediya-Janar Gusau ya ce tun bayan da kotun ta samu Seaman Abbas da laifukan ake tuhumarsa ne aka sallame shi daga aiki a ranar 7 ga watan Fabarairun 2023, sai dai an ci gaba da yi masa ɗaurin talala har zuwa lokacin da aka amince da hukuncin.
Ya ce ɗaya daga cikin laifukan da aka tuhumi Seaman Abbas ne suka janyo aka rage masa muƙami yayin da ragowar biyun kuma suka janyo masa abun kunya na sallama daga aiki.
“Tun bayan yanke masa wannan hukuncin ne aka ci gaba da yi masa ɗaurin talala a Barikin Soji na Mogadishu da ke Abuja har zuwa lokacin da Babban Hafsan Sojin Ruwa zai amince da hukuncin.
“Duk wasu bayanai yayin shari’ar da aka naɗa an miƙa wa Babbar Hedikwatar Tsaro ta Kasa a ranar 27 ga watan Yunin 2023, daga bisani ita ma Hedikwatar Dakarun Sojin Ruwa aka miƙa mata rahoton a ranar 8 ga watan Agustan 2023.
“Amma sai a ranar 19 ga watan Satumban 2024 ne Babban Hafsan Sojin Ruwa ya amince sannan ya tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Seaman Abbas,” in ji Birgediya-Janar Gusau.
‘Seaman Abbas ba ya fama da ta taɓin hankali’
Gusau ya musanta jita-jitar cewa an yi wa Seaman Abbas shari’a alhali yana fama da taɓin hankali.
Dangane da batun cewa Seaman Abbas yana fama da taɓin hankali, Gusau ya ce “muna da cikakken rahoto kan duk wasu gwaje-gwaje da aka yi masa a asibiti kuma kowane sakamako ya nuna lafiyarsa ƙalau.
“Mun samu shaida daga Cibiyar Lafiya ta Tarayya wadda ta tabbatar mana cewa yana da ƙoshin lafiyar da zai iya fuskantar shari’a.
“Ya ziyarci asibitoci daban-daban kuma dukkan asibitocin sun tabbatar da cewa yana da ƙoshin lafiyar da zai iya fuskantar shari’a.
“A dalilin ziyarar asibiti da ya riƙa yi akai-akai ne aka rushe kotun farko da ta fara zama kan tuhumar da ake yi masa domin ba shi dama da isasshen lokacin da zai ga likita.
“Amma duk sakamakon gwaje-gwajen da aka yi masa sun nuna yana da ƙoshin lafiyar da zai fuskanci shari’a”, a cewar Birgediya-Janar Gusau.
Ya ƙara da cewa, “babu laifi don an karɓe bindigar Seaman Abbas kamar yadda Ogansa ya yi.
“Duk wani Oga da yake da shakku kan ɗaya daga cikin yaransa, yana da damar ɗaukar mataki ba sai an jira ya aikata wani laifi ko ma ya kashe wani ba sannan a ce za a karɓe bindigarsa.
“Wannan bindiga mallakar Gwamnatin Nijeriya ce kuma mallakin Rundunar Sojin Nijeriya ce.
“Saboda haka duk lokaci da buƙata ta taso, kowane jami’i yana da damar da zai je wurin adana makamai ya sanya hannu sannan ya karɓi makami.
“Amma da zarar ogan da jami’i yake ƙarƙashinsa ya daina yarda da kai, yana da damar da zai ce ka dawo da wannan makami, idan kuma ka bijire sai a karɓe da ƙarfin tuwo.
Da yake ƙarin haske kan yadda tun farko da kaya tsakanin Abbas da ogansa, Birgediya-Janar Gusau ya ce Seaman Abbas ya riƙa nuna rashin ɗa’a a lokacin da ogansa yake tsakar gabatar musu da jawabi a filin fareti.
Ya ce Seaman Abbas ya bijere wa duk wasu umarni da ogansa ya ba shi ciki har da ƙin kai kansa ɗakin da ake ajiye sojojin da suka aikata laifi.
Matashiya
Makonni biyu da suka gabata ne dai a cikin wani faifan bidiyo, Hussaina matar Abbas ta bayyana cewa an gana masa uƙubar da ta wuce misali.
Hussaina ta bayyana ne a wani shiri na gidan talabijin na ‘Brekete Family’, inda a ciki ta bayyana wasu zarge-zargen cewa ba a yi wa mijinta da ma su iyalansa ɗin adalci ba.
Matar sojan wadda ake kira Maman Shahid, ta bayyana cewa mijin nata ya samu saɓani ne da wani babban hafsan soja, inda tun a lokacin aka kama shi, aka tsare, kuma a cewarta kusan shekara shida ke nan yana tsare.