An kori Shugaban jam’iyyar kwamunisanci kan bushashar Naira miliyan 41 a bikin auren dansa

An sauke Shugaban Jam’iyyar Kwamunisanci ta wani kauye da ke kasar Sin, bayan da dansa ya yi bushashar Dala dubu 260, wato kimanin Naira miliyan 41,600,000 a bikin aurensa, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.Kamfanin Dillancin Labarai na dinhua, ya bayyana cewa Hukumar Ladabtarwa da ke birnin Beijin, ta yanke hukunci a gundumar […]

An kori Shugaban jam’iyyar kwamunisanci kan bushashar Naira miliyan 41 a bikin auren dansa
An kori Shugaban jam’iyyar kwamunisanci kan bushashar Naira miliyan 41 a bikin auren dansa

An sauke Shugaban Jam’iyyar Kwamunisanci ta wani kauye da ke kasar Sin, bayan da dansa ya yi bushashar Dala dubu 260, wato kimanin Naira miliyan 41,600,000 a bikin aurensa, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.
Kamfanin Dillancin Labarai na dinhua, ya bayyana cewa Hukumar Ladabtarwa da ke birnin Beijin, ta yanke hukunci a gundumar Chaoyang, a ranar Talatar da ta gabata, in data samu Mista Ma Lindiang, wani mataimakin Darakta na jam’iyyar kwamunisanci, da ke kauyen kingheying da laifin almubazzaranci a bikin auren dansa. Shugaban jam’iyyar ya yi bushashar ne a daidai lokacin da Shugabancin jam’iyyar na kasa baki daya, ya gargadin jami’an jam’iyyar da su guji almubazzaranci don gudun tunzura mutane.
Duk da cewa hukumar ladaftarwar ba ta samu hujjar da ta nuna cewa Ma ya yi amfani da kudin al’umma ba, ta bayyana cewa almubazzaranci ya saba wa ka’idojin jam’iyyar.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan