An kori shugabannin kananan hukumomi saboda rashin sa takunkumi
An kori wasu Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Yobe saboda rashin sanya takunkumin kariyar cutar COVID-19 a wurin taro. Shugabannin rikon kananan kukumomin sun gamu da gamonsu ne a wurin mataimakin gwamnan jihar wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar, a wurin kaddamar da kwamitin kula da tsaftar muhallin yankunansu. Ya kori duk […]
An kori wasu Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Yobe saboda rashin sanya takunkumin kariyar cutar COVID-19 a wurin taro.
Shugabannin rikon kananan kukumomin sun gamu da gamonsu ne a wurin mataimakin gwamnan jihar wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar a jihar, a wurin kaddamar da kwamitin kula da tsaftar muhallin yankunansu.
Ya kori duk marasa takunkumi daga dakin taron da aka yi a gidan gwamnatin jihar, domin “Ba za ku bata kokarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi ba na kare mutane daga COVID-19”.
Ya nuna takaicin cewa maimakon su zama abin koyi, shugabannin wadanda yawancinsu Darektocin Kula da Ma’aikata ne a kananan hukumomi sun bige da saba dokokin kariyar cutar.
Don haka ya ce, “Zan dakatar da taron nan idan har a matsayinku na jagorori ba za ku bi umarni mai sauki ba kan kiyaye COVID-19”.